Labarai
Kungiyar Miyetti Allah Ta Yi Allah-wadai Da Kisan Shugabanta A Jihar Katsina
Hedikwatar Kungiyar Miyetti Allah ta Kasa ta yi Allah-wadai da kisan shugaban kungiyar reshen jihar Katsina da aka zaba a watannin baya, Alhaji Sirajo Ahmadu Mairana, a kauyen Mainasara da ke karamar hukumar Kusada.
A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar na kasa, Baba Othman Ngelzarma, ya ce an kuma yi garkuwa da wasu daga cikin iyalan marigayin.
Ya bayyana kisan a matsayin daya daga cikin illar da ake yi wa jama’a, biyo bayan tabarbarewar tsaro a yankunan Kankara, da ya addabi Arewa maso yammacin kasar nan.
Baba Othman ya yi kira ga gwamnatin Jihar Katsina da sauran hukumomin tsaro da su binciki wannan kisa domin gano wadanda suka aikata danyen aikin.
Watanni uku da suka wuce ne aka zabi Alhaji Sirajo Ahmadu Mairana a matsayin sabon shugaban kungiyar ta Miyetti Allah reshen jihar Katsina.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai23 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
