Labarai
Gwamnan Jihar Nasarawa Ya Rusa Majalisar Zartaswar Jihar
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya rusa majalisar zartaswar jihar nan take.
Gwamnan ya kuma sallami sakataren gwamnatin jihar Barista Mohammed Uban Doma Aliyu daga mukaminsa.
Ya sanar da hakan ne yayin taron majalisar zartarwar na gaggawa da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Lafiya, babban birnin jihar.
Ya umurci dukkan kwamishinonin da su mika al’amuran ma’aikatunsu ga manyan sakatarori, yayin da shi ma sakataren gwamnatin zai mika nasa ayyukan su ga babban sakatare mai kula da harkokin majalisar zartaswar jihar.
Gwamna Abdullahi Sule ya yabawa ‘yan majalisar zartaswar da sakataren gwamnatin jihar, bisa yadda suka yi aiki a gwamnatinsa.
Ya kuma bayyana jajircewarsu wajen gudanar da ayyukansu a matsayin abin yabawa, inda ya yi fatan samun nasara a ayyukansu na gaba.
A jawabin da ya yi a madadin sauran kwamishinonin, kwamishinan shari’a kuma babban lauyan jihar Barista Labaran Shu’aibu Magaji, ya godewa gwamnan bisa damar da aka basu na yin aiki a gwamnatinsa.
Daga Aliyu Muraki
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai24 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
