Labarai
Hukumar Alhazai Ta Jihar Kaduna Ta Fara Biyan Rarar Kudade Ga Alhazan 2023
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna ta fara biyan Naira 61,080 ga mahajjata 6,239 kowannensu, da suka yi aikin Hajji daga jihar a shekarar 2023.
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Yunusa Mohammed Abdullahi ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa kowane mahajjaci zai karbi kudi naira 61,080, kuma za a shigar da wadannan kudade kai tsaye cikin asusun ajiyar maniyyatan da abin ya shafa.
“Hukumar ta karbi wadannan kudaden ne daga hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON)”. Inji sanarwar.
“NAHCON ta bayyana cewa an mayar da kudaden ne sakamakon katsewar wutar lantarki a lokacin da Alhazai suka yi zaman Muna, lamarin da ya shafi na’urorin sanyaya daki, da kuma kawo cikas ga mahajjata”.
“Za mu yi duk mai yiwuwa don tabbatar da ganin an biya mahajjatan ta asusun bankinsu don gujewa matsala,” inji Shugaban Hukumar, Malam Salihu S. Abubakar, a wani taro da jami’an Alhazai na kananan hukumomin.
Sanarwar ta yi kira ga Alhazan da abin ya shafa da har yanzu ba su mika bayanansu ba da su tuntubi jami’an karamar hukumarsu domin a tantance su .
Abubuwan da ake buƙata don tantancewar sun haɗa da fasfo na tafiya da bayanan asusun banki.
Shugaban Hukumar, Malam Salihu S. Abubakar, ya bukaci jami’an hukumar da su tabbatar da bin ka’idoji bisa gaskiya da amana.
Adamu Yusuf
-
Labarai4 days agoJigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz
-
Labarai5 days agoTsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi
-
Labarai5 days agoNamadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027
-
Labarai5 days agoYankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari
-
Labarai4 days agoMajalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
-
Labarai3 days agoNamadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa
-
Labarai2 days agoKano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
-
Labarai3 days agoShugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus
