Labarai
An Yi Jana’izar Farfesa Yusuf Sa’idu Da ‘Yan Bindiga Suka Kashe
An gudanar da jana’izar mataimakin shugaban jami’ar Usman Danfodio da ke Sakkwato, Farfesa Yusuf Sa’idu, wanda ‘ƴan bindiga suka halaka a ranar Litinin.
Daya daga cikin abokan marigayin, Farfesa Bella Bada ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai.
Ya ce an yi jana’izar ne jim kaɗan bayan isowar gawar zuwa Sakkwato a yau Talata.
A jiya Litinin jami’ar ta Usman Danfodio ta fitar da sanarwa, wadda ke cewa an kashe malamin ne a kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Sakkwato inda yake aiki.
Hakan ya faru ne a ranar da gwamnonin jihohin arewa maso yammacin Najeriya, ciki har da Sakkwato suka buɗe wani taron yini biyu kan matsalar tsaron da ake addabar yankin.
Sakkwato na cikin jihohin Najeriya waɗanda ke fama da matsalar ƴan bindiga masu kisa da garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa.
Lamarin ya haifar da asarar rayuka da gurgunta tattalin arziƙi tare da tarwatsa mutane daga muhallansu.
A lokacin buɗe taron da gwamnonin jihon ke yi a birnin Katsina, Sarkin Musulmin Najeriya, Sa’ad Abubakar III ya ce “matuƙar ba a mayar da hankali ba, matsalar tsaron za ta kwashe gomman shekaru tana addabar yankin”.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
