Labarai
Gwamna Abba Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Kawo Ƙarshen Faɗan Daba A Kano
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya umarci jami’an tsaro da su kawo ƙarshen daba da masu tada zaune-tsaye a jihar.
Abba Kabir Yusuf, ya bayyana hakan ne a yayin taron majalisar zartarwa ta jihar (SEC) a Kano.
Gwamnan ya yi Allah-wadai da yadda ake samun tashe-tashen hankula a sanadin faɗan daba a wasu sassan jihar.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa ba za ta amince da duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiya da tsaro ba a jihar ba.
Ya ɗora wa alkalan jihar alhakin zartar da hukuncin waɗanda suke tsare cikin gaggawa da adalci.
Ya buƙaci hukumomin tsaro da su mayar da hankali wajen kare rayuka da dukiyoyi.
Kazalika, Yusuf ya buƙaci jama’ar jihar da su bai wa gwamnatinsa gudunmawa, sannan su kasance masu kiyaye doka da oda a jihar.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
