Connect with us

Labarai

Gwamna Namadi Ya Bada Goron Sallah Ga Alhazan Jihar Jigawa

Published

on

Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya bada Riyal 100  a matsayin goron Sallah ga  mahajjata jihar su  1,298.

Amirul Hajj na jihar kuma mai martaba Sarkin Hadejia Dr. Adamu Abubakar Make ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci masaukin Alhazai a Makkah.

Sarkin ya bayyana cewa, an dauki matakin ne don rage wahalhalun da Alhazai suka fuskanta a sakamakon dala 400 da aka ba su ta kudin guzuri saboda matsalar tashin Dala.

Ya yi kira ga maniyyatan da su yi addu’o’in samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar da kasa baki daya.

 

Dakta Adamu Abubakar Maje ya kuma yabawa dan jaridan nan na tawagar manema labarai ta jihar, Alhaji Abba Sa’idu Limawa wanda ya tsinci kudaden kasashen waje a Madina kuma ya mayar da ga  hukumar Alhazai ta kasa NAHCON,  ta hannun hukumar alhazai ta jihar Jigawa.

Shi ma da yake nasa jawabin babban daraktan hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ya yabawa mahajjatan bisa bin ka’idojin da aka gindaya na masarautar Saudiyya.

Ya yi kira ga maniyyatan da kada su wuce nauyin kilogiram  8 a jakar su ta   hannu da kuma kilogiram 32 a babbar jaka.

Wasu daga cikin Alhazan da suka zanta da gidan rediyon Najeriya sun godewa Gwamna Namadi bisa wannan karamci da aka yi musu, sannan sun yi alkawarin ci gaba da zama jakadu nagari ga jihar yayin da suke kasa mai tsarki.

A baya dai Gwamna Namadi ya biya Naira miliyan daya ga kowane maniyyacin aikin Hajjin 2024.

Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa,  tawagar gwamnatin da ta raka Amirul Hajj ya hada da mataimakin kakakin majalisar jiha, shugaban kwamitin majalisar kan aikin hajji da dai sauransu.

 

Usman Muhammad Zaria

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai1 week ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara