Labarai
Jirgin Farko Na Alhazan Najeriya Ya Sauka Birnin Kebbi Da Yammacin Asabar
Rukunin farko na alhazan jihar Kebbi, ya sauka filin jirgin saman Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi da yammacin Asabar.
Jirgin mai suna flynas da ya taso daga filin jirgin sama na Sarki Abdul-Aziz da ke Jidda, ya sauka Kebbi ne da misalin karfe 9 da minti 42 na dare tare da alhazai 410 ciki har da jami’an hukumar jin dadin alhazai ta jihar.
Dukkanin mahajjatan suna cikin koshin lafiya sai dai wasu da suke fama da mura sakamakon shan abubuwa masu sanyi davoda da matsanancin zafi da sanyi da tari suka shafa sakamakon shan ruwan sanyi da na’urar sanyaya iska a lokacin da suke kasa mai tsarki.
Kashi na farko da suka isa Najeriya su ne na farko da aka fara jigilar su daga Najeriya zuwa Saudiyya a ranar 15 ga watan Mayun 2024 a yayin kaddamar da jirgin da mataimakin shugaban kasa Kashim Shattima ya yi a Birnin Kebbi, jihar Kebbi.
Abdullahi Tukur
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
