Labarai
Gwamnatin Jigawa Ta Gwangwaje Kungiyoyin Wasanni Da Kyaututtuka
Kwamishinan yada labarai matasa da wasanni na jihar Jigawa, Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bada kyautuka ga kungiyoyin wasanni da suka yi fice a gasar wasan cikar Gwamna Mallam Umar Namadi shekara guda akan karagar mulki.
An gudanar da bikin karramawar ne a dakin taro na Sir Ahmadu Bello dake Dutse.
Alhaji Sagir Musa Ahmed yace bada kyautukan na daga cikin alkawarin da Gwamna Umar Namadi ya yi a lokacin wasan karshe na murnar cikar gwamna shekara guda a kan karagar mulki.
An bada kyautar naira miliyan 4 ga kulob din kwallon kafa na Dutse da ya zo na farko, sai kulob din Birnin Kudu wanda ya yi na biyu da ya samu kyautar naira miliyan 3.
Lautai united wadda tazo na uku ta sami kyautar naira miliyan 2.
Kazalika, an bada kyautuka ga zakarun wasannin langa da dambe da kokuwa da wasan kwando da wasan kwallon hannu da dai sauran su.
A jawabinsa, kwamishina Sagir Musa Ahmed ya ce hakan ya nuna cewar an dawo da ruhin wasanni a Jigawa
Ya kuma yi bayani akan kokarin da ake na habbaka harkokin wasanni a jihar.
Ya ce suna tattaunawa da kwamishinonin ilmi domin yin amfani da makarantu wajen farfado da harkar wasanni.
Usman Mohammed Zaria
-
Labarai4 days agoJigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz
-
Labarai5 days agoTsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi
-
Labarai5 days agoNamadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027
-
Labarai4 days agoMajalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
-
Labarai5 days agoYankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari
-
Labarai3 days agoNamadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa
-
Labarai2 days agoKano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
-
Labarai3 days agoShugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus
