Labarai
Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Aikin Ginin Filin Jiragen Sama Na Gusau
Ministan Sufurin Jiragen Sama, Dr. Festus Keyamo, ya kaddamar da aikin gina filin jiragen sama na Gusau a jihar Zamfara, kan kudi naira biliyan sittin da biyu.
A lokacin da yake kaddamar da aikin, Ministan ya bayyana filin jiragen saman a matsayin abin alfahari ga jihar da ma kasa baki daya.
Ya bayyana cewa, aikin filin jirgin zai kara habbaka harkokin noma da kasuwanci na al’ummar jihar yana mai cewa, amfanin noma da kasuwanci a jihar ko shakka babu za su ci gaba da bunkasa filin jirgin.
Festus Kiyamo ya ci gaba da bayyana cewa, tuni tawagar kwararru ta fara aiki ba dare ba rana don ganin cewa aikin ya tabbata, ya kara da cewa, gwamnatin tarayya za ta ba da duk wani tallafi da gudummawar da ake bukata domin samun nasarar aikin.
A nasa jawabin, Gwamna Dauda Lawal ya ce za a ba da kulawar da ta dace domin samun nasarar kammala filin jirgin cikin wa’adin da aka kayyade da yarjejeniyar kwangilar watanni 32.
Ya ce idan aka kammala aikin zai taimaka wajen samar da ayyukan yi da kuma rage radadin talauci, ba ma a jihar kadai ba har da kasa baki daya.
Sani Haruna Dutsinma
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai21 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai23 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
