Connect with us

Labarai

Gwamnatin Jigawa Ta Gwangwaje Kungiyoyin Wasanni Da Kyaututtuka

Published

on

Kwamishinan yada labarai  matasa da wasanni na jihar Jigawa, Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bada kyautuka ga kungiyoyin wasanni da suka yi fice a gasar wasan cikar Gwamna Mallam Umar Namadi shekara guda akan karagar mulki.

An gudanar da bikin karramawar ne a dakin taro na Sir Ahmadu Bello dake Dutse.

Alhaji Sagir Musa Ahmed yace bada kyautukan na daga cikin alkawarin da Gwamna Umar Namadi ya yi a lokacin wasan karshe na murnar cikar gwamna shekara guda a kan karagar mulki.

An bada kyautar naira miliyan 4 ga kulob din kwallon kafa na Dutse da ya zo na farko,  sai kulob din Birnin Kudu wanda ya yi na biyu da ya samu kyautar naira miliyan 3.

Lautai united wadda tazo na uku ta sami kyautar naira miliyan 2.

Kazalika, an bada kyautuka ga zakarun wasannin langa da dambe da kokuwa da wasan kwando da wasan kwallon hannu da dai sauran su.

A jawabinsa, kwamishina Sagir Musa Ahmed ya ce hakan ya nuna cewar an dawo da ruhin wasanni a Jigawa

Ya kuma yi bayani akan kokarin da ake na habbaka  harkokin wasanni a jihar.

Ya ce suna tattaunawa da kwamishinonin ilmi domin yin amfani da makarantu wajen farfado da harkar wasanni.

 

Usman Mohammed Zaria

Labarai

Labarai1 hour ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi1 week ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Mafi Shahara