Kasuwanci
Shugaba Bola Tonibu Ya Gana Da Shugaban Afrika Ta Kudu
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wata ganawar sirri da takwaransa na Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, a birnin Johannesburg, yau Alhamis.
A tattaunawar da suka yi kafin ganawar ta sirri a birnin wanda shi ne mafi girma a Afirka ta Kudu Shugaba Ramaphosa ya gode wa Shugaba Tinubu kan yadda ya halarci bikin sake rantsar da shi, shugaban kasa a wa’adi na biyu wanda aka yi jiya Laraba.
A yayin ganawar Tinubu ya sheda wa Ramaphosa cewa bayanan da jawabin Ramaphosa na lokacin rantsuwar kama aiki ya tabo yawancin matsalolin da kasashen Afirka suke fuskanta, kuma ya nuna cewa akwai bukatar shugabanni su hada kai domin samar da mafita.
A ranar Juma’a 14 ga watan Yuni ne aka sake zaben Mista ramaphosa a matsayin shugaban kasar a wa’adi na biyu na tsawon shekara biyar, bayan yarjejeniyar da jam’iyyarsa ta ANC (African National Congress) ta kulla da DA (Democratic Alliance)
Bello Wakili/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
