Kasuwanci
Kalaman Gwamnan Zamfara A Kan Jami’an Tsaro Basu Dace Ba
Wata kungiyar siyasar Zamfara a jam’iyyar APC Youth wing mobilization vanguard, ta bayyana damuwarta kan kalaman da Gwamna Dauda Lawal ya yi a gidan talabijin na kasa kan abubuwan da suka shafi tsaro a jihar.
A wata sanarwa da shugaban kungiyar Alh Ashiru Tukur ya raba wa manema labarai a Gusau, ya ce kalaman Gwamnan ba shi da tushe balle makama idan aka yi la’akari da sadaukarwar da jami’an tsaro daban-daban suke yi wajen yaki da rashin tsaro a jihar.
Hakazalika ta yi Allah wadai da abin ya kira kai hare-hare na rashin kishin kasa da na baki da ake kaiwa ministan tsaro na kasa da sojoji da ke da hannu a yunkurin da ake na dakile tashe-tashen hankula a jihar.
Sanarwar ta kuma yi kira ga Gwamnan da ya tashi tsaye wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar kamar yadda ya yi alkawari a lokacin da ya hau mulki.
Sanarwar ta yaba wa karamin ministan tsaro, Dakta Bello Mohammed Matawalle bisa yadda ya taimaka wajen inganta aikin soji da ayyukan da ake gani a jihar da sauran jihohin da ke makwabtaka da su.
Don haka ta yi kira ga Gwamna Dauda Lawal da ya kara kaimi wajen bayar da goyon baya, ba da hadin kai da kuma hada kai da hukumomin tsaro da ke aiki a jihar da kuma wannan wasan zargi.
Bello Mujtaba/ Staff/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
