Connect with us

Labarai

An Bai Wa Alhazan Jihar Naija Tabbacin Samun Kyakkyawar Kulawa Yayin Aikin Hajji

Published

on

Alhazan jihar Neja sun samu tabbacin kyautata walwala da jin dadinsu yayin da suke kasa mai tsarki  don gudanar da aikin hajjin bana.

Mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Yakubu Garba ya ba da wannan tabbacin ga jirgin karshe na jigilar alhazan jihar  daga filin jirgin sama na Bola Ahmad Tinubu da ke Minna zuwa birnin Madina na kasar Saudiyya.

Kwamared Yakubu Garba ya ce  gwamnatin jihar Naija a karkashin jagorancin Gwamna Mohammed Umar Bago Alhazan jihar ta yi tanadi na musamman ga Alhazan domin samun  kyakkyawar kulawar da ta da ce yayin gudanar da aikin hajjin bana ba tare da wata matsala ba.

Ya kuma yi kira ga Mahajjatan da su yi addu’a ga jihar Neja da kasa baki daya, domin fatan Allah Ya warware dukkan kalubalen da ake fuskanta.

A nasa jawabin Amirul Hajj na jihar kuma Sarkin Kagara, Ahmed Garba Gunna Attahiru na biyu, ya bayyana jin dadinsa bisa goyon baya da hadin kan da  Gwamna Umar Bago ya ba su domin gudanar da aikinsu.

Ya ce a nasu bangaren mambobin tawagarsa za su yi duk mai yiwuwa don tabbatar da ganin sun sauke nauyin da aka daura musu.

 

Aliyu Lawal

 

Labarai

Labarai1 hour ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi1 week ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Mafi Shahara