Ilimi
Mai Martaba Sarkin Gumel Ya Jaddada Kudirinsa Na Tallafawa Makarantun Tsangaya Da Islamiyya
Mai Martaba Sarkin Gumel da ke Jihar Jigawa, Alhaji Ahmad Muhammad Sani ya sake jaddada kudirinsa na ci gaba da tallafawa makarantun tsangaya da na islamiya domin samar da mahaddata Alqur’ani a fadin masarautarsa.
Mai Martaban ya bayyana hakan yayin bikin yaye mahaddata Alqur’ani 27 da makarantar marigayi Malam Habu Gade ta gudanar karo na 12 a garin Gumel.
Ya ce masarautarsa tana maraba da makarantun tsangaya da na islamiya domin ci gaba da hidimtawa Alqur’ani mai tsarki.
Mai Martaba Sarkin wanda ya sami wakilcin Sa’in Gumel, Alhaji Sani Abdullahi ya bukaci iyaye da su tabbatar ‘Yayansu na zuwa makarantun mahammadiya da na zamani domin samun ilmi.
Tun da farko a nasa jawabin, shugaban makarantar Malam Lawan Abubakar Gade ya ce wannan shine karo na 12 da makarantar ta yaye mahaddata Alqur’ani maza da mata tun kafuwarta a shekarar 1970.
Yana mai mika godiygrsa ga Gwamnatin jihar Jigawa bisa sanya makarantar a cikin tsarin makarantun Tsangaya tare da godewa Mai martaba sarki bisa goyon baya da ya ke bawa makarantar.
A jawabinsa a madadin iyayen yara Malam Hassan Magaji ya ce za su ci gaba da sa ido akan zuwa ‘yayansu makaranta akan lokaci.
Usman Mohammed Zaria
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
