Connect with us

Labarai

Mun Shirya Tsaf Don Fara Jigilar Alhazan Jihar Jigawa- Ahmad Labbo

Published

on

Hukumar Jin dadin alhazai ta Jihar Jigawa ta bukaci maniyyatan Jihar su zama cikin shiri domin ana dab da fara jigilar su zuwa kasa mai tsarki don aikin hajjin bana.

Hukumar ta kuma bayyana cewar tuni ta tura Jami’anta da za su tarbi alhazan a kasar Saudi Arabia.

Darakta Janar na Hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana haka a zantawarsa tare da Wakilinmu Usman Mohammed Zaria dake Dutse Babban birnin Jihar.

Ya bayyana cewar shirye-shirye sun kammala domin sun ziyarci filin sauka da tashin jirage na Nuhu Muhammadu Sunusi dake Dutse domin tabbatar da al’amura sun daidaita kamar yadda aka tsara.

Alhaji Ahmed Umar Labbo ya kara da cewar, a zancen da ake yi yanzu an fara tsaftace tare da feshin maganin sauro a sansanin alhazai dake fanisau domin samun walwalar alhazai wajen tantance su.

Game da batun tsaro kuwa, yana mai cewar tuni hukumar ta zauna tare da tattauna da jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki domin samar da tsaro ga alhazai tun daga kananan hukumomin su da sansanin alhazai da kuma filin jirgin da ke Dutse.

Daraktan ya ce tuni wasu daga cikin jami’an hukumar na Jidda, wasu kuma a Madina,  yayin da wasu ke garin Makka don tabbatar da ganin Alhazan sun sami kyakkyawar kulawar da ta dace da zarar sun isa kasa mai tsarki.

Labbo, yayi nuni da cewar a kowanne Jirgi akwai rukunin jami’an lafiya da ‘yan jaridu da Malamai masu fadakarwa da za su kasance tare da Alhazai  akan kowace gaba ta aikin hajji.

A don haka, ya bukaci maniyyatan jihar da su kasance jakadu na gari tare da kiyaye dokokin  kasar nan da na Saudi Arabia, wajen gujewa  ddaukr abubuwan da aka haramta ttafya da su.

Darekta Janar din ya kuma yabawa Gwamna Umar Namadi bisa hadin kai da goyon bayan da yake baiwa hukumar don kwalliya ta ci gaba da biyan kudin sabulu.

 

Usman Mohammed Zaria

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara