Labarai
Hajjin Bana: Gwamnan Zamfara Ya Kaddamar Da Jigilar Maniyyatan Jihar
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya kaddamar da jigilar maniyyata kashin farko zuwa kasa mai tsarki domin gudanar da aikin hajjin 2024.
Gwamna Dauda Lawal wanda ya kaddamar da fara gudanar da aikin a sansanin Alhazai na jihar da ke Samaru Gusau, babban birnin jihar, ya kuma yi kira ga alhazan da su bin dokokin Saudiyya sau da kafa, kuma su guji duk wani abu da zai iya bata sunan su da na jiharsu da ma Najeriya baki daya.
Dauda Lawal ya kuma bukace su da su yi amfani da kudaden su yadda ya dace, tare da gujewa sayayya barkatai.
Ya sanar da bayar da kykyautar Dala dari ga kowane mahajjaci daga jihar, inda ya kara da cewa, ita ma mai dakinsa Hajia Huriya Dauda Lawal ta shiryabayar da irin wannan kyauta ga Alhazan.
Gwamnan ya kuma yi kira ga maniyyatan jihar da su yi addu’ar samun dauwamammen zaman lafiya a jihar Zamfara da yankin Arewa da ma Najeriya baki daya.
Tun da farko, a jawabinsa na maraba, Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Zamfara, Malam Musa Mallaha, ya ce maniyyata dubu daya da dari bakwai da sha biyu ne ake sa ran za su yi aikin Hajjin bana.
Jirgin farko na jihar ya kunshi mahajjatan daga kananan hukumomi hudu na jihar wadanda suka hada da Bakura, Bukuyum, Gummi da Shinkafafi, kuma ana sa ran zai tashi daga filin jirgin saman Sultan Abubakar III da sanyin safiyar yau Laraba 29 ga watan Mayu, 2024.
Sani Haruna Dutsinma
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
