Connect with us

Labarai

Gwamnatin Jihar Kano Za Ta Yi Gwajin Tarin Fuka Kyauta Ga Kananan Yara

Published

on

Gwamnatin jihar Kano za ta yi wa yara 6,000 a cibiyoyin lafiya 1,346 gwajin cutar tarin fuka kyauta.

Kwamishinan lafiya na jihar Dr. Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da manema labarai domin tunawa da makon gwajin cutar tarin fuka na kasa na shekarar 2024.

A cewarsa bikin ya kasance na musamman, domin an hada shi da sauran ayyukan kiwon lafiya kamar su abinci mai gina jiki,  cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV, wayar da kan al’umma, da sauransu.

Kwamishinan ya bayyana cutar tarin fuka a matsayin cuta mai saurin yaduwa, wacce ke bin iska kuma gaba daya tana shafar huhu da ma wasu  gabobin jiki.

Dr. Abubakar ya yi nuni da cewa, ana iya kamuwa da ita daga mai dauke da nau’in cutar zuwa wani wanda akasari ta hanyar tari, atishawa, magana ko dariya, wanda alamomin ta suka hada da tari na tsawon makonni biyu ko fiye da zazzabi mai alaka da shi ko kuma ba tare da shi ba, rage nauyi ko zufa cikin dare.

Wasu alamomin da ke da alaƙa a jikin yara na iya haɗawa da rashun kuzari, fitar jini yayin tari, da kumburin wasu gabobi da rashin cin abinci“. Inji shi.

Ya ci gaba da cewa yaran da ke dauke da cutar tarin fuka ko kuma wadanda ba a kula da su ba za su iya yada ta zuwa kusan mutane 10 zuwa 15 a cikin shekara guda, inda ya bukaci iyaye da su kai ’ya’yansu don yin gwajin cutar kyauta.

Hakkin ‘ya’yanmu ne a yi musu gwajin cutar tarin fuka, ya zama wajibi a matsayinmu na iyaye mu tabbatar da lafiya da walwalar ‘ya’yanmu kuma ya zama wajibi  ga gwamnatin jihar Kano ta samar da ababen  da za su dakile yaduwar cutar”.

Dokta Abubakar ya ci gaba da cewa, gwamnatin jihar Kano tare da hadin gwiwar ma’aikatar lafiya ta tarayya ta shirya shirin yaki da cutar tarin fuka da kuturta, inda aka samar da kayan aiki da magunguna da kwararrun ma’aikata da sauran kayayyakin da ake bukata.

Ciki har da injinan yin hoton jiki na X-Ray guda 20 da  na gwajin kwayoyin cututtuka wato microscopes  guda 250, da na’urorin gwajin cutar HIV da ta tarin fuka, da sauransu.

Kwamishinan ya bukaci ‘yan jarida da su kara himma wajen wayar da kan jama’a game da illar cutar tarin fuka da kuma muhimmancin kai  ‘ya’yansu domin yi musu gwaji da kuma yi musu magani.

 

Khadijah Aliyu

 

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai1 week ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara