Connect with us

Ilimi

Ana Binciken Zargin Rashin Biyan Wani Sarki Mai Shekaru 101 Albashi A Jihar Kwara

Published

on

 

 

Gwamnatin jihar Kwara ta ce ta fara gudanar da bincike kan zargin rashin biyan albashi da wasu kudade na tsawon shekaru 21 ga wani basaraken gargajiya na Jebba mai shekaru 101 a karamar hukumar Moro ta jihar, Oba Abdulkadir Alabi Adebara.

 

Da yake zantawa da manema labarai yayin taron manema labarai da ma’aikatar sadarwa da dabaru ta jihar ta shirya a Ilorin, kwamishinan kananan hukumomi da al’amuran masarautu na jihar, Abubakar Bata, ya ce gwamnatin jihar ce ke binciken lamarin.

 

Ya ce gwamnatin jihar tana kan gaba a kan batun masarautar Jebba da nufin samar da mafita mai dorewa a kan lamarin.

 

Basaraken, wanda gwamnatin Alhaji Mohammed Lawal ta daga darajjar Sarkin zuwa mai darajja ta 3 a shekaru 20 da suka gabata (16 ga Mayu, 2003), sai dai gwamnatocin da suka biyo baya sun rage masa darajarsa.

 

A wani labari na daban kwamishiniyar ilimi da ci gaban bil’adama ta jihar, Hajiya Sa’adatu Modibbo Kawu, ta ce gwamnatin jihar ta biya naira miliyan dubu 7 a matsayin nata kaso domin bunkasa ilimi a jihar.

 

Ta ce ayyukan da gwamnatin jihar ke yi a fannin bunkasa ilimi da horar da malamai ya janyo raguwar rashin zuwa makaranta da kashi hamsin cikin dari a jihar.

 

A nata jawabin kwamishiniyar ci gaban al’umma ta jihar, Afolashade Kemi, ta ce gwamnati ta kwashe mabarata daga birnin Ilorin.

 

Kwamishinar ta bayyana cewa an kwashe su cikin shekara guda da ta gabata wanda a lokacin samamen anyi zargin cewa mafi akasarin mabaratan an same su da muggan makamai kamar bindigu da wukake da laya da sauran muggan makamai.

 

COV/ALI MUHAMMAD RABIU/Wababe

 

 

 

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai1 week ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara