Connect with us

Labarai

An Samar Da Masauki Kusa Da Harami Ga Alhazan Jihar Jigawa

Published

on

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa  ta samar da katafaren masauki  kusa da Masallacin Harami da ke birnin Makkah na kasar Saudiyya ga Alhazan jihar da za su sauke farali a bana.

Babban Daraktan hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana hakan ga wakilin gidan rediyon Najeriya a Dutse babban birnin jihar.

Ya ce hukumar ta samar da masauki mai daraja da zai yi gogayya da na sauran kasashen duniya kusa da masallacin Harami, domin baiwa Alhazan jihar damar zuwa masallacin ba tare da wata wahala ba.

Ya kuma bayyana cewa, Gwamna Umar Namadi  ya kudiri aniyar bai wa  hukumar duk wani tallafin da ya dace domin  samun damar kulawa da Alhazan jihar yadda ya kamata.

Dangane da ciyarwa yayi aikin Hajji kuwa, Ahmed Labbo ya bayyana cewa, hukumar ta kulla yarjejeniya da wani kamfani don samar da ingantaccen abinci ga  Alhazan jihar  yayin gudanar da aikin Hajjin.

Ya ce, hukumar na da kwarin gwiwar cewa kamfanin zai cimma yarjejeniyar da suka kulla.

Shugaban ya yi nuni da cewa, za su rika bada kulawa ta musamman ga mahajjatan da ke fama da lalurar rashin lafiya don ganin su ma an samar musu abincin da ya dace da su.

Yayin da ya yaba wa ma’aikatan hukumar kan kwazon su, ya kuma  umarce su da su sake sadaukar da kansu don ganin an samu nasarar aikin Hajjin bana.

Labbo ya bayyana godiya ga gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Umar Namadi da kuma hukumar Alhazai ta kasa NAHCON bisa goyon bayan  da suke  bai wa hukumar jin dadin alhazai ta jihar jigawa.

Usman Muhammad Zaria

Labarai

Labarai1 hour ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi1 week ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Mafi Shahara