Labarai
An Gudanar Da Taron Bita Kan Dashen Koda A Kano
Shugaban Jami’ar Bayero da ke Kano Farfesa Sagir Adamu, ya ce asibitin koyarwa na Aminu Kano ya gudanar da dashen koda sama da dari daya daga shekarar 2002 zuwa yanzu.
Farfesa Sagir ya bayyana hakan ne a yayin wani taron bitar dashen koda na yini uku da Asusun Tallafawa Manyan Makarantu na Kasa TETFUND ya shirya a asibitin koyarwa na Aminu Kano (AKTH).
Shugaban jami’ar wanda mataimakinsa na sashen gudanarwa Farfesa Mahmud Sani ya wakilce shi, ya bayyana cewa, Asibitin Aminu Kano na daya daga cikin asibitocin koyarwa na Arewa da suka fara aikin dashen koda shekaru 20 da suka gabata.
Ya yabawa Asusun na TETFUND bisa kaddamar da taron shirin a AKTH tare fatan ganin dorewarsa da kuma fadada shi zuwa wasu asibitocin.

A jawabinsa Babban Daraktan Kula da Lafiya na asibitin, Farfesa Umar Gajida, ya yi nuni da cewa Asusun TETFUND ya yi ayyuka da dama a fannin dashen Koda.
Shugaban ’yan kwangilar da suka samar da kayan aikin dakin gwaje-gwaje Alhaji Umar Ali, ya jaddada cewa an kashe sama da Naira miliyan dari biyu don sayan kayan aikin dashen Koda.
Wasu daga cikin mahalarta taron da suka zanta da gidan rediyon Najeriya sun yi alkawarin yin amfani da ilimin da suka samu ta hanyar da ta dace.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa an zabo mahalarta taron ne daga asibitocin koyarwa guda shida a fadin jihohin Kano da Bauchi da Filato da Maiduguri da Abuja da kuma Kaduna, inda za a yi dashen koda har guda uku a karshen taron bitar domin likitocin su kara fahimtar aikin dashen.
Khadija Aliyu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
