Ilimi
Sasantawa ce Jigon Kowane Irin Zaman Lafiya – Dr Joseph

Cibiyar tabbatar da zaman lafiya da sasantawa ta ce tana ganawa da manyan abokan hulda da masu ruwa da tsaki a duk fadin kasar a wani yunkuri na samar da zaman lafiya ba tare da nuna banbancin addini ko kabalancin ba.
Babban daraktan cibiyar, Dr. Joseph Ochogwu ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a jihar Sokoto.
Mista Joseph Ochogwu ya ce cibiyar da ke karkashin ma’aikatar harkokin waje ta tarayya a halin yanzu tana hada kungiyoyin farar hula, hukumomin tsaro, malamai, kungiyoyin addini a kokarinta na tattauna hanyoyin da ake bukata da kuma samar da hanyoyi domin samun dauwamammen zaman lafiya a kasa.
Shugaban ya ce an dauki matakin ne da nufin inganta fahimtar juna tsakanin jama’a da dukkan gwamnatocin jihohi da nufin samar da ribar dimokuradiyya don samun ci gaba mai dorewa.
Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta bukaci goyon bayan jama’a domin ba gwamnati damar samar da manufofi da tsare-tsare da suka shafi ci gaban tattalin arziki da tsaro a kasar nan.
Mista Joseph Ochogwu ya kara da cewa, za a iya cimma hakan ta hanyar samar da zaman lafiya da sasanta rikici tsakanin gwamnatocin jihohi da al’ummomi a fadin kasar nan.
Ya kara da cewa shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu yana ajandar muhimman abubuwa guda takwas da suka ta’allaka gaba daya kan zaman lafiya, tsaro da ci gaban tattalin arziki.
NASIR MALALI/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
