Labarai
Gwamnan Kano Ya Mika Sunayen Sabbin Kwamishinoni 2 Ga Majalisa Domin Tantancewa
Daga Khadijah Aliyu
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya zaɓi mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, da Balarabe Sa’idu Gani domin naɗa su a matsayin kwamishinoni a jihar.
Gwamnan ya aika da sunayensu zuwa Majalisar Dokokin Jihar Kano domin tantancewa da tabbatar da naɗinsu.
Shugaban Majalisar, Jibril Isma’il Falgore ne ya sanar da zaɓen nasu yayin zaman majalisar, bayan karanta wasiƙar da gwamnan ya aika.
Ya ce za a gudanar da tantance ’yan takarar a ranar Talata, 3 ga Nuwamban 2026, da ƙarfe 10 na safe.
Shugaban Majalisar ya bayyana cewa za a gudanar da aikin tantancewar bisa tanadin Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya.
Rediyon Najeriya ya rawaito cewa Sanusi Bature Dawakin Tofa ne a halin yanzu mai magana da yawun Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Wannan na zuwa ne mako guda bayan Majalisar ta tantance tare da tabbatar da naɗin mutane shida a matsayin kwamishinoni, ciki har da tsohon kwamishina Aminu Ibrahim Tsanyawa, da tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano, Farfesa Sani Lawan.
Fassara: Safiyah Abdulkadir
-
Labarai4 days agoJigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz
-
Labarai5 days agoTsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi
-
Labarai5 days agoNamadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027
-
Labarai5 days agoYankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari
-
Labarai4 days agoMajalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
-
Labarai3 days agoNamadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa
-
Labarai2 days agoKano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
-
Labarai2 days agoShugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus
