Labarai
REMASAB Ta Bayyana Damuwarta Game Da Tsaftar Muhalli A Kano
Daga Khadijah Aliyu, Kano
Hukumar Kula da Shara da Tsaftar Muhalli ta Jihar Kano, REMASAB, ta ƙara tsaurara sa ido kan tsaftar muhalli a faɗin jihar, inda ta tura wata tawaga ta musamman domin duba manyan da ƙananan hanyoyi da kuma wasu muhimman wurare.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na REMASAB, Abubakar Ahmad, ya sanya wa hannu, inda ya ce an ɗauki matakin ne domin inganta tsaftar muhalli, sarrafa shara, yanayin magudanan ruwa da kuma tabbatar da bin ƙa’idojin tsaftar muhalli da aka gindaya.
Sanarwar ta ce an kuma ɗora wa tawagar alhakin sa ido kan ayyukan ma’aikatan REMASAB, domin tabbatar da cewa suna gudanar da ayyukan da aka ɗora musu cikin inganci da ƙwarewa, ciki har da amfani da kayan kariya na musamman.
A wani ɓangare na ayyukan da take gudanarwa a wurare daban-daban, tawagar sa ido ta ziyarci Gadar Dangi, inda ta duba yanayin tsaftar muhalli a yankin tare da nazarin ayyukan tsaftar da ake gudanarwa.
Hukumar ta ce binciken da aka gudanar ya gano cewa wasu maza, mata da yara sun mayar da yankin ƙarƙashin gadar da kuma kewayenta a matsayin wurin zama na wucin gadi.
REMASAB ta kuma ce an gano wasu sassan gadar da ake amfani da su wajen yin bayan gida a fili.
Hukumar ta bayyana cewa wannan yanayi na haifar da damuwa game da lafiyar jama’a, tsaftar muhalli da kuma tsaro, musamman ganin cewa wurin yana kusa da muhimman ababen more rayuwa na jama’a.
Ta yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su ɗauki matakin da ya dace cikin haɗin gwiwa domin magance matsalar cikin mutunta mutanen da abin ya shafa da tsari da kuma hanyar da za ta dore.
Hukumar ta kuma jaddada buƙatar kare wuraren jama’a da muhimman ababen more rayuwa daga ayyukan da ka iya yin illa ga lafiyar muhalli da tsaron jama’a.
Binciken na daga cikin ƙoƙarin da Manajan Daraktan REMASAB, Dakta Muhammad S. Khalil, ke yi na ƙarfafa sa ido kan ayyukan hukumar da inganta ayyukan sarrafa shara da kuma ɗaga matsayin tsaftar muhalli a faɗin Jihar Kano.
Hukumar ta buƙaci mazauna jihar da al’ummomi da sauran masu ruwa da tsaki da su ci gaba da tallafa wa ƙoƙarin tsaftar muhalli, ta hanyar tsaftace muhallinsu da amfani da wuraren da aka ware domin zubar da shara da kuma guje wa duk wasu ayyuka da ka iya haifar da lalacewar muhalli.
Fassara: Shafii Abubakar Wababe
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
