Labarai
Katsina: Dalibai 64 Sun Jikkata Bayan An Musu Rigakafin Cutar Tsargiya
Daga Isma’il Adamu
Aƙalla dalibai 64 na makarantar sakandaren kimiyya ta gwamnati da ke Batagarawa, a jihar Katsina, aka garzaya da su asibiti biyo bayan rigakafin cutar Tsargiya da jami’an lafiya suka musu.
Rahotanni sun bayyana cewa daliban sun yi fama da amai, ciwon ciki, jiri da rashin jin daɗin jiki, lamarin da ya sa mahukuntan makarantar garzayawa da su asibitin ƙashi na Amadi Rimi da kuma asibitin mata da yara na Turai Yar’Adua da ke Katsina.
Cutar Tsargiya, wacce aka fi sani da Bilharzia a Turance, cuta ce da ƙwayoyin cuta masu alaƙa da tsutsotsi ke haddasawa, kuma galibi ana kamuwa da ita ta hanyar hulɗa da gurbataccen ruwan sha ko na wasu hanyoyin ruwa.
Yayin da wasu jami’an asibitoci suka bayyana alamomin da daliban suka nuna a matsayin abubuwan da kan faru bayan shan maganin.
Wasu likitoci biyu da suka zanta da Rediyon Najeriya bisa sharaɗin ɓoye sunayensu, sun danganta lamarin da yiwuwar an ba daliban magani fiye da kima.
Ɗaya daga cikin likitocin ya ce ya ziyarci asibitin, inda ya ga dalibai da dama cikin mawuyacin hali.
Wani likita a asibitin Turai Yar’Adua kuwa, ya yi zargin cewa an ƙayyade adadin alluran maganin Praziquantel da za a ba daliban ne bisa tsayinsu, maimakon shekarunsu, lamarin da ya haifar da tambayoyi kan ko an bi ƙa’idojin bayar da maganin yadda ya kamata.
Wasu daliban sun bayyana cewa an ba su allura daga ɗaya zuwa huɗu, yayin da aka yi zargin cewa ba a sanar da iyayensu ba kafin ba su maganin.
Masana lafiya sun kuma nuna damuwa kan dalilin da ya sa ba a tantance lafiyar kowane dalibi ba kafin ba shi maganin ba. Sun jaddada muhimmancin yin binciken lafiya da ya dace domin tabbatar da buƙatar shan maganin da kuma tabbatar da cewa an ba da shi cikin aminci.
Binciken Rediyon Najeriya ya kuma nuna cewa an ba dalibai da dama maganin ne ba tare da sun ci abinci ba, bayan dawowarsu makaranta daga hutu da misalin ƙarfe 11 na safe. Dalibai da iyaye da aka zanta da su sun ce ba a ba daliban abinci ba kafin ko bayan shan allunan maganin.
A nata ɓangaren, ƙungiyar haɗin gwiwar ƙungiyoyin fararen hula ta jihar Katsina ta buƙaci gudanar da cikakken bincike kan lamarin, tana mai bayyana shi a matsayin babban yanayi na gaggawar lafiya.
Shugaban ƙungiyar, AbdurRahman Abdullahi, ya ce ya kamata hukumomin da abin ya shafa su binciki yadda aka bada maganin, ciki har da amfani da tsayi wajen ƙayyade adadinsa, yadda aka kula da batun abinci da kuma matakan da aka tanada domin magance yiwuwar illolin maganin.
Ya buƙaci ma’aikatun ilimin firamare da sakandare da na lafiya na jihar su gano hakikanin abin da ya faru, su tabbatar da duk wani sakaci da aka yi, sannan su ɗauki matakan da za su hana sake faruwar irin wannan lamari.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Katsina, SP Abubakar-Sadiq Aliyu, ya sanya wa hannu, rundunar ta tabbatar da faruwar lamarin, amma ta musanta rahotannin da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta na cewa wasu dalibai sun mutu.
Rundunar ’yan sandan ta ce lamarin ya biyo bayan wani rahoton zargin barkewar cutar Tsargiya da shugaban makarantar, Sanusi Maude, ya kai asibitin makarantar. A cewar sanarwar, jami’an lafiya sun ba dalibai sama da 700 maganin Praziquantel, a rukuni biyu.
Rukunin farko da aka ba maganin ranar Juma’a, 24 ga Oktoba, ba su nuna wata matsala ba, yayin da daliban rukuni na biyu, waɗanda aka ba maganin ranar Litinin, suka fara nuna alamomin rashin lafiya. Yawancin daliban da abin ya shafa sun samu kulawar likitoci, kuma an sallame su daga asibiti.
Fassara: Safiyah Abdulkadir
-
Labarai4 days agoRundunar ‘Yan Sanda Ta Tabbatar da Rasuwar Sheikh Yahaya Masussuka
-
Labarai3 days agoSu Waye Suka Kashe Sheikh Yahaya Masussuka a Dutsin-Ma
-
Labarai3 days agoBa Za a Amince da Raba Kafa a Zabukan 2027 Ba — Ministan Yada Labarai
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Tabbatar Da Nadin Kwamishinoni Shida
-
Kasuwanci3 days agoTsohon Ministan Harkokin Waje Gambari Ya Ƙalubalanci Matasa Kan Zaman Lafiya Da Gina Ƙasa
-
Kasuwanci3 days agoNijeriya Za Ta Fara Kera Makamai Da Kayayyakin Tsaro Masu Yawa
-
Labarai2 days agoMutane Aƙalla 64 Sun Mutu a Haɗarin Jiragen Ƙasa a Sifaniya
-
Labarai2 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Amince da Kudirin Kafa ’Yan Sandan Jiha
