Labarai
Gwamnatin Jigawa Za Ta Biya Diyar Naira Miliyan 982 Ga Wadanda Aikin Hanya Ya Shafa
Daga Usman Muhammad
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da biyan sama da naira miliyan 982 a matsayin diyya ga masu gidaje da gine-ginen da aikin gina hanyar garin Kafin Hausa zai shafa.
Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana hakan ga manema labarai jim kadan bayan taron majalisar zartarwar jihar da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Dutse.
Ya ce amincewar ta nuna yadda gwamnatin Gwamna Umar Namadi ta himmatu wajen bunkasa birane da karkara, wanda ke daga cikin muhimman manufofin shirin gwamnatin jihar.
A cewarsa, aikin hanyar garin Kafin Hausa na da nufin inganta ababen more rayuwa da kuma saukaka zirga-zirga tsakanin sassa daban-daban na jihar.
Sagir ya bayyana cewa, kammala aikin zai inganta harkokin sufuri a yankin, rage lokacin tafiya, bunkasa kasuwanci da kuma inganta rayuwar al’ummar garin.
Kwamishinan ya bukaci mazauna yankin da masu gidajen da aikin ya shafa da su ci gaba da ba Ma’aikatar Ayyuka, masu aikin awo da ’yan kwangila cikakken hadin kai domin tabbatar da kammala aikin cikin sauki kuma akan lokaci.
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da aiwatar da ayyukan raya karkara da birane domin bunkasa tattalin arziki da jin dadin al’ummar Jigawa.
Fassara: Safiyah Abdulkadir
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
