Connect with us

Labarai

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Published

on

Daga Nasir Malali 

Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto mutane 23 da aka yi garkuwa da su, tare da kama wasu mutane huɗu da ake zargin mambobin ƙungiyar ta’addanci ta Lakurawa  a Jihar Sakkwato.

Jami’in Yaɗa Labarai na Rundunar, Laftanar Janar Aliyu Danja, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce dakarun sun samu nasarori a wasu ayyuka daban-daban da suka gudanar a sassan jihar, da nufin dakile ayyukan ‘yan ta’adda.

A ranar 20 ga watan Satumban 2026, dakarun sun kai dauki a harin da ‘yan ta’adda suka kai Sabon Gari a Ƙaramar Hukumar Wurno, inda suka yi musayar wuta da maharan tare da tilasta musu ja da baya. Dakarun sun kuma ceto mutane shida da aka yi garkuwa da su, yayin da aka kai wani farar hula da ya samu raunin harbin bindiga asibiti.

A wani samame, dakarun sun yi wa ‘yan ta’adda kwanton bauna a kusa da Chabe Biyu da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Birni, bayan samun bayanan sirri kan yunƙurin da suke yi na ratsa hanyar Sabon Birni zuwa Takatsaba. Haka kuma, an ceto wasu mutane 17 da aka yi garkuwa da su bayan artabu da ‘yan ta’adda a hanyar Isa zuwa Kwanar Isa zuwa Shinkafi. Ɗaya daga cikin waɗanda aka ceto ya samu karaya an kuma  kai shi Babban Asibitin Isa.

A Ƙaramar Hukumar Illela kuwa, dakarun sun kama mutane huɗu da ake zargin mambobin Lakurawa ne, bayan samun bayanan sirri kan yadda suke tafiya da garken shanun da aka sace daga ƙauyen Sarma zuwa Illela. An kuma kwato shanu shida a yayin samamen.

Sanarwar ta ce nasarorin sun nuna tasirin ayyukan dakarun da ke amfani da bayanan sirri wajen dakile ayyukan ta’addanci, ceto mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma hana ‘yan ta’adda damar zirga-zirga cikin sauƙi a yankin da ake gudanar da ayyukan haɗin gwiwa.

Fassara: Safiyah Abdulkadir 

Labarai

Labarai7 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai10 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai7 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai7 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai7 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai7 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai7 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai7 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara