Connect with us

Labarai

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Published

on

Daga Isma’il Adamu, Katsina

Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta Jihar Katsina, SUBEB, sun ƙaddamar da shirin Skills4Girls, wata sana’o’I domin yara mata da nufin bai wa ’yan mata matasa 35,000 a jihar Katsina dabarun sana’o’in dogaro da kai da kuma kasuwanci.

Shirin, wanda ake gwajinsa a Najeriya a jihar Katsina kaɗai, an ƙaddamar da shi ne ta hanyar wani taron haɗin gwiwar tsara shirin da ya samu halartar ’yan mata matasa daga ƙananan hukumomin Katsina, Funtua, Kaita da Dutsi.

Da take jawabi a wajen taron, ƙwararriyar UNICEF kan bunƙasa matasa, Ngozi Izuora-Songu, ta ce an tsara shirin ne domin tabbatar da cewa ’yan mata sun samu ƙwarewar da za ta amfani rayuwarsu fiye da abin da suke koya a aji, tare da ba su damar bayar da gudunmawa mai kyau ga al’ummominsu.

Ta ce babban manufar shirin ita ce tabbatar da cewa ’yan matan sun samu ƙwarewar da za ta taimaka musu wajen samun abin dogaro da kai da kuma bayar da gagarumar gudunmawa ga al’umma.

A cewarta, shirin zai mayar da hankali ne kan gina ƙwarewa a fannoni uku, waɗanda suka haɗa da ƙwarewar samun aikin yi, kasuwanci da kuma iya samar da abubuwan amfani da kuma mayar da wani ɓangare na abin da aka samu ga al’umma.

Izuora-Songu ta bayyana cewa, yayin da wasu shirye-shirye kamar Girls Education Project (GEP) da REACH suka mayar da hankali, a wani ɓangare, kan ci gaba da karatu da kammala makaranta, shirin Skills4Girls zai gina ne bisa nasarorin da aka samu daga waɗannan shirye-shirye, tare da ƙara ba ’yan mata damar dogaro da kansu ta fuskar tattalin arziki.

Ta ce ana gudanar da tantance ƙwarewar ’yan matan ne domin gano bambance-bambancen da ke tsakaninsu da kuma irin baiwar da kowannensu yake da ita.

Ta ƙara da cewa ba sa son dogaro da zato wajen tsara shirin, inda za a kuma gudanar da taron haɗin gwiwar tsara shirin tare da ’yan matan domin jin ra’ayoyinsu game da irin sana’o’i da kasuwancin da suke son koyon su ko shiga.

A cewarta, hakan zai taimaka wajen tsara shirin da zai dace da buƙatunsu da kuma yanayin muhallin da suke rayuwa.

Izuora-Songu ta bayyana cewa shirin zai gudana daga shekarar 2026 zuwa 2029, kuma ana sa ran zai amfani ’yan mata 35,000 masu shekaru tsakanin 10 zuwa 19 a ƙananan hukumomin Katsina, Funtua, Kaita da Dutsi.

Ta kuma ce ’yan mata masu lalura ta musamman za su samu damar shiga shirin domin tabbatar da cewa kowa ya samu dama ta bai ɗaya wajen koyon ƙwarewar da za ta taimaka masa a rayuwa.

Bugu da ƙari, shirin zai kuma shigar da samari da matasa maza 7,500, da kuma iyaye, masu ba da shawara, masu horarwa da shugabannin al’umma 5,000, abin da zai kai jimillar waɗanda za su amfana da horon zuwa 47,500.

A nasa jawabin, Shugaban Hukumar Ilimin Firamare ta Jihar Katsina, Dakta Kabir Gafia, ya ce hukumar za ta taka rawar da ya kamata wajen tabbatar da nasarar shirin.

Dakta Gafia ya ce gwamnatin Jihar Katsina ta yi matuƙar maraba da shirin, saboda manufofinsa sun yi daidai da ajandar gwamnatin jihar mai taken “Building Your Future”, wato gina makomar ku.

Ya ce gwamnatin jihar ta kasance tana koyar da matasa da ’yan mata sana’o’i daban-daban domin su samu damar dogaro da kansu.

Ya lissafa wasu daga cikin sana’o’in da shirin zai mayar da hankali a kansu, da suka haɗa da sarrafay man shafawa da sabulu da sabulun wanke-wanke da turare, da kuma ɗinki, saka, gyaran wayoyin hannu da na’urorin lantarki, da kuma fasahar sadarwa da kwamfuta (ICT), da sauransu.

Dakta Gafia ya buƙaci ’yan mata matasa da sauran waɗanda shirin ya shafa da su yi cikakken amfani da damar da shirin ya samar domin inganta rayuwarsu da makomarsu.

Fassara: Shafii Abubakar Wababe

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara