Connect with us

Labarai

‘Yan Fashin Tekun Somalia Sun Sako Jirgin Bangladesh Bayan Karbar Kudin Fansa

Published

on

‘Yan fashin tekun Somalia sun sako wani jirgin ruwan dakon kaya mai tutar Bangladesh tare da ma’aikatansa 23 a yau lahadi, bayan da masu jirgin suka biya kudin fansa.

Jirgin ruwan MV Abdullah wanda ke jigilar kusan tan dubu hamsin da biyar  na kwal daga kasar  Mozambique zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa, wasu gungun ‘yan fashin teku da dama ne suka shiga da shi a nisan kilomita 1,000 daga gabar tekun Somalia wata guda da ya gabata.

“Mun cimma yarjejeniya da ‘yan fashin,” in ji Mizanul Islam, na kamfanin SR Shipping, mallakin kungiyar KSRM ta Bangladesh.

A cikin watan Maris, dakarun sa kai na  India sun kutsa cikin jirgin ruwan Malta MV Ruen, wanda ‘yan fashin tekun Somalia ke rike da shi tun watan Disambar 2023. Wannan dai shi ne nasara na farko da aka samu na fashin teku a gabar tekun Somalia tun shekara ta 2017.

Ma’aikatan jirgin su 17, ‘yan Bama mutum  9, da ‘yan Bulgaria 7 da kuma dan Angola guda, an ceto su ba tare da wani rauni ba, sannan an kai ‘yan fashin 35 zuwa Bombay na kasar India domin gurfanar da su a gaban Kuliya.

 

Labarai

Labarai2 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi1 week ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Mafi Shahara