Labarai
Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 835 Don Sayen Kayan Agajin Gaggawa Saboda Ambaliya
Daga Usman Muhammad
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da sayen kayayyakin agajin gaggawa na shirin tunkarar ambaliya da mayar da martani na shekarar 2026, kan kuɗi sama da naira miliyan 835.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana haka ga Rediyon Najeriya a Dutse.
Ya ce, kayayyakin da aka amince a saya sun haɗa da muhimman kayan abinci na gaggawa, kayan sawa, da kuma kayan gini, domin tabbatar da gaggawar taimako idan ambaliya ta auku a sassan da ke cikin haɗarin ambaliya a jihar.
Ya bayyana cewa, amincewar majalisar zartarwa ga Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jiha (SEMA) na da nufin tabbatar da cewa za a tanadi waɗannan kayan agaji a wurare masu muhimmanci domin a iya kai su cikin gaggawa duk lokacin da bukata ta taso.
Ya ƙara da cewa, kayan abinci za su taimaka wajen magance bukatun gaggawa na abinci ga mutanen da ambaliya ta raba da muhallansu, yayin da kayan sawa da na gini za su bayar da muhimmin tallafi ga iyalan da iftila’in ambaliya ya shafa.
Sagir ya jaddada cewa, gwamnatin jihar ta yi kira ga mazauna jihar, musamman waɗanda ke zaune a yankunan da ke fuskantar haɗarin ambaliya, da su ci gaba da bin shawarwarin tsaro da hukumomin da abin ya shafa ke bayarwa.
Ya kuma bukaci jama’a da su nuna haɗin kai da goyon baya ga hukumomin agajin gaggawa idan irin wannan iftila’i ya faru.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
