Labarai
Shugaba Tinubu Ya Rantsar da Sabbin Ministocin Lantarki da Harkokin Waje
Daga Bello Wakili
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Mista Joseph Olasunkanmi Tegbe a matsayin Ministan Wutar Lantarki, da kuma Ambasada Sola Enikanolaiye a matsayin Minista a Ma’aikatar Harkokin Ƙasashen Waje.
An gudanar da bikin rantsarwar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda iyalan ministocin da manyan jami’an gwamnati suka halarta.
Nadin nasu ya biyo bayan murabus ɗin tsofaffin ministocin Wutar Lantarki da Harkokin Waje, inda Majalisar Dattawa ta tabbatar da sababbin ministocin a watan Mayun 2026.
Tegbe, wanda ya fito daga Jihar Oyo, ƙwararren masanin tattalin arziƙi ne kuma injiniya, ya kuma yi aiki a KPMG da wasu manyan cibiyoyi a Najeriya da ƙasashen waje. Ya taka muhimmiyar rawa wajen gyare-gyaren tattalin arziƙi da makamashi a matakin gwamnati da kamfanoni.
Shi kuwa Ambasada Enikanolaiye, ɗan Jihar Kogi, ƙwararren jami’in diflomasiyya ne da ya shafe shekaru 35 yana aiki a Ma’aikatar Harkokin Waje. Ya yi aiki a ofisoshin jakadancin Najeriya a ƙasashe da dama kamar Canada, Ingila, da India, inda ya riƙe manyan mukamai kafin ritayarsa.
Bayan ritaya, ya ci gaba da aiki a matsayin mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin ƙasashen waje kafin wannan sabon naɗin nasa.
Shugaba Tinubu ya bayyana kwarin gwiwa cewa sabbin ministocin za su taimaka wajen inganta aiki a muhimman fannoni biyu na wuta da hulɗar ƙasa da ƙasa.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai7 days agoGwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya
