Labarai
‘Yan Sanda Sun Kama Mutane 345 Tare da Kwato Makamai 270 a Kano
Daga Abdullahi Jalaluddeen
Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Kano ta ce ta kama mutane 345 tare da kwato makamai masu haɗari guda 270 a wani samame na kwanaki uku da aka gudanar a faɗin jihar domin yaƙi da daba, fataucin miyagun ƙwayoyi da sauran laifuka.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Bompai. Ya ce an gudanar da aikin tsakanin 5 zuwa 7 ga watan Yuni a dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar.
Ya ce samamen ya mayar da hankali ne kan maboyar masu laifi, wuraren da ake yawan aikata laifuka da cibiyoyin rarraba miyagun ƙwayoyi, bisa umarnin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda na ƙara kaimi wajen yaƙi da laifuka.
Bakori ya ce daga cikin waɗanda aka kama akwai masu daba, masu fataucin miyagun ƙwayoyi da kuma mutanen da aka samu da makamai masu haɗari, inda ake ci gaba da bincike a kansu kafin gurfanar da su a kotu.
Ya ƙara da cewa jami’an rundunar sun kwato wuƙaƙe, adduna, sanduna da sauran kayayyakin da ake zargin ana amfani da su wajen aikata tashin hankali.
Haka kuma, rundunar ta kama ɗimbin miyagun ƙwayoyi da suka haɗa da tabar wiwi, ƙwayoyin Exol da kuma wani sinadari mai haɗari da aka fi sani da “Suck and Die”.
Kwamishinan ya danganta nasarar da aka samu da Operation Kukan Kura da kuma sabon kula da Manyan Laifuka na Tashin Hankali (VCRU), waɗanda suka taimaka wajen inganta sintiri, tattara bayanan sirri da gaggauta kai dauki.
Ya jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da yaƙi da laifuka a Kano, tare da yabawa gwamnatin jihar da al’umma bisa haɗin kan da suke bai wa jami’an tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
