Labarai
An Kama Tsohon Jami’in Gwamnati da Wasu 5 Kan Zargin Garkuwa da Yaro a Katsina
Daga Isma’il Adamu
Tsohon Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamna Dikko Radda kan Shirin Ci gaban Al’umma, Nura Aliyu, ya shiga hannun ’yan sanda bisa zargin jagorantar gungun masu garkuwa da mutane da suka sace wani yaro ɗan shekara 8 tare da karɓar Naira miliyan 17 a matsayin kuɗin fansa.
Wata sanarwa daga kakakin rundunar ’yan sanda, DSP Abubakar Sadiq, ta ce an kama Aliyu tare da wasu mutum biyar a cikin birnin Katsina, yayin da ake cigaba da neman mutum na bakwairuwa a jallo.
Rahotonni sun bayyana cewa an sace yaron ne a ranar 13 ga watan Mayun 2026, da misalin ƙarfe 6:00 na yamma yayin da yake dawowa daga makarantar Islamiyya.
Masu garkuwar sun fara neman Naira miliyan 50 a matsayin fansa, amma daga bisani aka cimma matsaya a kan Naira miliyan 17 da aka biya kafin sakin yaron.
Jami’an sashen musamman na yaki da manyan laifuka (VCRU) sun ce sun fara bincike nan take bayan samun rahoto, inda suka bi sahihan bayanan sirri har suka kama waɗanda ake zargi.
Waɗanda aka kama sun haɗa da Nura Aliyu mai shekara 39, wanda ake zargi a matsayin shugaban gungun, tare da Abubakar Aminu, da Ibrahim Muhammad, da Iliyasu Sani, da Abubakar Muhammad da kuma Abdullahi Isma’il.
An ce an gano tsabar kudi Naira miliyan 7 da rabi a maboyarsu, tare da wata mota ƙirar Peugeot 307 da kuma babur guda ɗaya.
Binciken farko ya nuna cewa waɗanda ake zargin sun amsa laifinsu tare da bayyana wani mutum mai suna “Abdul” a matsayin cikon da bakwai.
A halin yanzu, ana ci gaba da farautar wanda ya tsere tare da tabbatar da cewa za a gurfanar da waɗanda aka kama a kotu.
A gefe guda, Gwamnatin Jihar Katsina ta nesanta kanta da Nura Aliyu, tana mai cewa an kore shi ne daga aiki saboda zargin karkatar da kayan tallafi, ba murabus ba kamar yadda wasu rahotanni suka bayyana.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
