Connect with us

Labarai

Yaƙi da Daba: Gwamnatin Kano Ta Fara Shirin Horas da Matasa Dubu Ɗaya

Published

on

Daga Khadijah Aliyu 

Gwamnatin Jihar Kano ta kammala shirye-shiryen horas da matasa dubu ɗaya kan dabarun inganta rayuwa da sana’o’in dogaro da kai domin bunƙasa rayuwarsu da ci gaban al’umma.

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Ibrahim Waiya ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar aiki da ya kai Cibiyar Tsaro ta Jihar Kano da ke Gabasawa.

A cewarsa, shirin ya shafi matasan da suka rungumi tsarin Safe Corridor wanda gwamnatin jihar ta ƙaddamar a baya a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin  inganta makomar matasa.

Ibrahim Waiya ya ce gwamnatin jihar Kano na ci gaba da jajircewa wajen yaƙi da daba da kuma dakile rikice-rikicen siyasa a faɗin jihar.

Ya bayyana cewa an ware kusan naira miliyan 600 domin aiwatar da shirye-shiryen ƙarfafa matasa, inganta zaman lafiya da tabbatar da daidaiton zamantakewa.

A nasa jawabin, Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II wanda Sarkin Shanun Kano, Shehu Muhammad ya wakilta, ya yaba wa gwamnatin jihar bisa ƙoƙarinta na inganta zaman lafiya da haɗin kai a jihar Kano.

Shi ma da yake jawabi yayin ziyarar, fitaccen ɗan kasuwar Kano, Alhaji Sabi’u Bako, ya yabawa gwamnati bisa bada fifiko a ci gaban matasa, yana mai cewa shirin zai taimaka wajen rage rashin zaman lafiyar matasa da ƙarfafa zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Ya kuma yi alƙawarin haɗa kan ‘yan kasuwar Kano domin tallafa wa shirin, don tabbatar da dorewar zaman lafiya da ci gaba.

Wakilan Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa da sauran masu ruwa da tsaki sun halarci ziyarar.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara