Fasaha
Cibiyar Kuɗi Ta Yi Alkawarin Haɗin Gwiwa
Cibiyar koyar da dabarun tsara harkokin kuɗi domin dorewar tattalin arziki ta sake jaddada aniyarta na haɗa kai da gwamnati da majalisun dokoki domin inganta yadda ake tafiyar da kuɗaɗen jama’a a Najeriya.
Daraktan Janar na cibiyar, Farfesa Abdullahi Ya’u, ya bayyana haka yayin taron masu tsara harkokin kuɗi na Afirka da aka gudanar a Abuja. Ya ce cibiyar na zuba jari sosai wajen bincike da ci gaba domin bunƙasa harkokin kuɗi a matakin ƙasa da na ƙananan al’umma.
Ya ce cibiyar na ƙaddamar da wani babban shiri mai suna “ Shirin Bada Fifiko akan ‘yan kasa, wanda ya ƙunshi buƙatu da gibin ci gaba da al’ummomin ƙananan hukumomi 774 na ƙasar nan ke da su.
Farfesa Abdullahi Ya’u ya bayyana cewa an gudanar da bincike mai zurfi domin gano matsaloli da buƙatun al’umma a dukkan ƙananan hukumomin ƙasar. Ya ce manufar shirin ita ce tabbatar da shugabanni sun cika alƙawuran da suka ɗauka ga jama’a.
A cewarsa, shekaru da dama ana gudanar da zaɓe tare da alƙawuran baka ba tare da rubutattun yarjejeniyoyi tsakanin shugabanni da al’umma ba. Ya ce wannan sabon tsarin zai bai wa jama’a damar sanin ayyukan da ‘yan siyasa suka yi alkawarin aiwatarwa idan sun samu mulki.
Daraktan Janar ɗin ya ce ƙwararru na da muhimmiyar rawa wajen sake fasalin yadda ake raba albarkatu da tafiyar da su domin cigaban ƙasa. Ya ƙara da cewa za a samar da takardun ga dukkan ƙananan hukumomi domin jama’a su amfana da su.
Ya kuma bayyana cewa ana son kowace al’umma ta cimma matsaya da masu neman muƙami kan irin ayyukan da za su aiwatar idan suka hau mulki, domin kawo ƙarshen alƙawuran da ba sa haifar da sakamako.
Masu halartar taron sun nuna kwarin gwiwa cewa cibiyar za ta taimaka wajen inganta rayuwar ‘yan Najeriya. Haka kuma, mai kula da cibiyar, Husaini Sani Abubakar, ya yi alƙawarin haɗa ƙananan sana’o’i cikin tsarin tattalin arziki domin bunƙasa arzikin ƙasa.
Bashir Mayere/Abuja
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
