Labarai
Tsohon Shugaban NPHCDA Ya Janye Daga Takarar Gwamnan APC, Ya Mara Wa Wadada Baya
Tsohon Babban Daraktan Hukumar Bunƙasa Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Ƙasa, Dr. Faisal Shu’aib, ya sanar da janyewarsa daga takarar gwamnan Jihar Nasarawa a karkashin jam’iyyar APC.
Dr. Faisal Shu’aib ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Lafia, inda ya ce ya yanke shawarar janyewa daga takarar ne bisa yarjejeniyar da masu neman takarar suka yi cewa duk wanda aka zaba daga cikinsu, sauran za su mara masa baya domin tabbatar da nasarar jam’iyyar mai mulki.
Ya kuma sanar da hade tsarin yakin neman zabensa da na Sanata Ahmed Aliyu Wadada domin mara masa baya.
A cewarsa, daga yau ya janye daga takarar gwamna, kuma zai ci gaba da goyon bayan Sanata Ahmed Aliyu Wadada a matsayin wanda ya fi dacewa ya gaji Gwamna Abdullahi Sule a zaben shekarar 2027.
Dr. Faisal Shu’aib ya ce a matsayinsu na Musulmi sun yi imani cewa mulki daga Allah yake zuwa, yana bayar da shi ga wanda Ya so a lokacin da Ya so, kuma yanzu lokaci ne na Sanata Ahmed Aliyu Wadada.
Tsohon shugaban na National Primary Health Care Development Agency ya kuma yaba wa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da Gwamna Abdullahi Sule bisa irin salon shugabanci mai kyau da suke aiwatarwa.
Haka kuma ya yi alkawarin bayar da cikakken goyon baya domin tabbatar da nasarar jam’iyyar APC tun daga matakin mazaba har zuwa na ƙasa baki ɗaya.
Aliyu Muraki/Lafiya
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
