Labarai
Hukumar Alhazai ta Kasa ta Kai Ziyarar Gani-da-Ido Jihar Jigawa
Daga Usman Muhammad Zaria
Hukumar Alhazai ta Ƙasa NAHCON ta kai ziyarar gani da ido a filin jirgin sama da sansanin Alhazai na Jihar Jigawa a cigaba da shirye-shiryen aikin Hajjin shekarar 2026.
Tawagar wadda Kwamishinan NAHCON na shiyyar Arewa maso Yamma, Sheikh Muhammad Bin Uthman ya jagoranta, ta samu tarba daga Daraktan Gudanarwa da Kudi na Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Alhaji Muhammad Umar Sambo, a madadin shugaban hukumar.

A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Alhaji Habibu Yusuf Babura ya rabawa manema labarai, ya ce tawagar ta duba wuraren tantance Alhazai a sansanin.
A cewarsa, tawagar ta kuma duba kayayyakin aiki da ke Filin Jirgin Sama na Nuhu Muhammadu Sunusi da ke Dutse, babban birnin jihar.

Sheikh Bin Uthman ya bayyana gamsuwarsa da yadda jihar ta shirya wajen karɓa da tantance dukkan Maniyyata kafin tashinsu zuwa ƙasa mai tsarki.
Ya yabawa Gwamnatin Jihar Jigawa bisa ci gaba da goyon baya da jajircewa wajen kula da jin daɗin Alhazai, musamman wajen samar da masauki, kula da lafiya da sauran harkokin tafiyarsu zuwa mai tsarki.

A shekarar 2025, an yaba wa Jihar Jigawa bisa kyakkyawan tsari da gudanar da aikin Hajji, inda tawagar NAHCON ta nuna kyakkyawan fata cewa jihar za ta ci gaba da riƙe wannan kambu a shekarar 2026.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
