Labarai
Majalisar Dattawa ta jaddada haɗin kai don bunƙasa wasanni a Najeriya
Majalisar Dattawa ta Najeriya ta sake jaddada aniyarta na haɗa kai da ƙwararrun masu ilimin harkokin wasanni domin dawo da ƙasar kan gaba a nahiyar Afirka.
Shugaban kwamitin Majalisar kan bunƙasa wasanni, Sanata Abdul Ningi, ya bayyana haka ne yayin tantance Mainasara Umar Illo wanda aka naɗa domin zama babban sakatare kuma shugaban cibiyar yaƙi da amfani da ƙwayoyi a wasanni ta Najeriya.
Ya ce akwai buƙatar a bai wa masu ƙwarewa dama domin inganta harkokin wasanni a ƙasar, tare da yabawa Bola Ahmed Tinubu kan ƙoƙarinsa na bunƙasa fannin.
Mambobin kwamitin sun nuna goyon bayansu ga naɗin Illo, suna fatan hakan zai taimaka wajen cimma burin bunƙasa wasanni a Najeriya.
Da yake mayar da martani, Mainasara Illo ya yi alƙawarin cewa idan aka tabbatar da shi, zai yi aiki tukuru wajen bunƙasa fannin wasanni domin samar da ayyukan yi da ci gaban tattalin arziki ga matasa.
Ya kuma ce zai yi aiki da hukumomi kamar nay aji da sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA domin tabbatar da gwaje-gwaje ga ‘yan wasa, ta yadda za su iya fafatawa a gasar ƙasa da ƙasa.
Illo ya ƙara da cewa cibiyar yaƙi da amfani da ƙwayoyi a wasanni na da matuƙar muhimmanci, amma tana buƙatar isasshen tallafi, inda ya buƙaci Majalisar Tarayya ta mara wa gwamnati baya wajen bunƙasa harkokin wasanni.
Bashir Mayere/Abuja
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
