Connect with us

Labarai

Shugaban Majalisar Dattawa Akpabio Ya Taya Musulmi Murnar Sallah

Published

on

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya taya al’ummar Musulmi a Najeriya murnar bikin Eid-el-Fitr, tare da kira ga tausayi, yafiya da haɗin kai yayin da Musulmi a duniya ke gudanar da wannan biki.

A cikin saƙon taya murna da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Honorabul Eseme Eyiboh ya sanyawa hannu, Akpabio ya yaba wa Musulmi kan nasarar kammala ibadar azumin watan Ramadan, yana mai ƙarfafa su da su ci gaba da ayyukan alheri kamar bayar da sadaka da nuna ƙauna ga juna.

Ya bayyana cewa wannan biki na Sallah na tunatar da al’umma muhimman darussa na tausayi, yafiya da haɗin kai da Eid-el-Fitr ke ɗauke da su.

Akpabio ya buƙaci al’ummar Musulmi da su tuna da muhimmancin jin ƙai, kyautatawa da karamci ga juna, musamman ga marasa galihu, yayin da suke kammala wannan ibada ta azumi da nazarin ruhaniya.

Ya ce, “Ina fatan ruhin Sallah zai ƙarfafa mu wajen bunƙasa tausayi, fahimtar juna, da kuma aiki tare domin samar da Najeriya mai adalci da zaman lafiya.”

A ƙarshe, Shugaban Majalisar Dattawan, a madadin iyalinsa, al’ummarsa, Majalisar Dattawa da kuma Majalisar Tarayya ta goma, ya yi wa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da dukkan Musulmi fatan murnar Sallah mai albarka, tare da addu’ar samun zaman lafiya, ci gaba da wadata a Najeriya da ma duniya baki ɗaya.

 

Bashir Mayere/Abuja

Labarai

Labarai2 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi1 week ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Mafi Shahara