Connect with us

Labarai

Hukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani

Published

on

Ayyukan ban ruwa a yankin Kogin Benuwe na fuskantar barazana sakamakon taruwar Laka da Yashi a kogin, lamarin da ke kara dakile karfin ruwan tare da toshe hanyoyin da yake kwarara.

Hukumar Kula da Kogin Benuwe (UBRBDA) ta bayyana a wata sanarwa cewa matsalar na ƙara tsananta, musamman ga al’ummomin da ke amfana da ruwan kogin,  ciki har da aikin noman rani da Geriyo, wanda aka dogaro da shi domin ayyukan ban ruwa.

Binciken da aka gudanar a ranar 2 ga watan Maris na shekarar 2026, da misalin ƙarfe 5 na yamma, ya nuna cewa matakin ruwa ya kai mita 1 da digo 43, yayin da yawan ruwan da ke kwarara ya kai  ma’aunin mita 64 a sakan guda, adadin da aka bayyana a matsayin mafi ƙaranci da aka samu a lokacin rani.

Masana sun yi gargadin cewa idan kwararar ruwa na raguwa matuka, taruwar laka kan ƙara tsananta matsalar, lamarin da ke haddasa raguwar zurfin ruwa, toshe hanyoyin shigar ruwa, rage ƙarfin gudun gudun ruwan, da kuma barazana ga wadatar shi domin ban ruwa.

Hukumar ta yi gargaɗin cewa idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba, matsalar na iya ƙara muni, tare da shafar wadatar ruwa da ayyukan noma a lokacin rani.

Domin shawo kan matsalar, an fara aikin zurfafa hanyoyin ruwan na musamman,  ƙarƙashin kulawar Shugaban Hukumar kuma Babban Jami’in Gudanarwa, Dakta Mahmud Sanusi Mohammed.

A cewar hukumar, aikin zai fi mayar da hankali ne a wuraren da laka ta fi taruwa domin dawo da kwararar ruwa yadda ya kamata, da sauƙaƙa zirga-zirgar ruwa, da kuma samar da ruwa domin ban ruwa ba tare da haddasa wata matsalar ba.

Jami’ai sun bayyana cewa wannan mataki ne na kariya da aka ɗauka bisa sahihan bayanai na kimiyya, maimakon a jira matsalar ta tsananta kafin ɗaukar mataki.

 Daga:Yusuf/Safiyah

Labarai

Labarai2 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi1 week ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Mafi Shahara