Labarai
Gwamnatin Tarayya Ta Faɗaɗa Rijistar Tallafin Jama’a Domin Tantance Masu Buƙata
Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa tare da ƙarfafa Rijistar Tallafin Jama’a ta Ƙasa National Social Register domin tabbatar da cewa an tantance gidaje marasa ƙarfi a faɗin ƙasar nan yadda ya kamata, an yi musu rajista, tare da haɗa su cikin tsare-tsaren kariya da tallafin zamantakewa.
Ministan Ma’aikatar Harkokin Jin-ƙai da Rage Talauci, Dakta Bernard Doro, ya bayyana haka a wajen ƙaddamar da rabon kayan tallafin abinci da na gina jiki ƙarƙashin Shirin Shugaban Ƙasa na Tallafin Abinci da Gina Jiki, wanda aka gudanar a Minna, Jihar Niger.
Dakta Bernard Doro ya ce ma’aikatar za ta yi aiki kafada da kafada da Gwamnatin Jihar Niger domin tabbatar da cewa an yi rajistar dukkan masu cin gajiyar shirin da mutanen da lamarin ya shafa a faɗin jihar, ta yadda za su cancanci shiga shirye-shiryen kariya da rage talauci na Gwamnatin Tarayya.
A cewarsa, Gwamnatin Tarayya ta himmatu wajen tabbatar da cewa samar da wadataccen abinci, rage talauci da kuma kare al’umma masu rauni sun kasance ginshiƙai a tsarin mulkinta, domin kada a bar kowane ɗan Najeriya mai buƙata a baya.
A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Niger, Mohammed Umar Bago, ya gode wa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa ci gaba da bai wa jihar goyon baya. Ya kuma yaba wa hukumomin tallafi da sauran masu ruwa da tsaki da suka bayar da gudunmawa.
Mohammed Umar Bago ya bayyana cewa Jihar Niger na da kusan kashi goma cikin ɗari na faɗin ƙasar Najeriya, lamarin da ke sa kula da tsaro a dukkan sassan jihar ya zama ƙalubale ba tare da cikakken goyon bayan Gwamnatin Tarayya ba. Ya kuma jaddada ‘yancin yara na zuwa makaranta, tare da kira ga haɗin gwiwar dukkan masu ruwa da tsaki domin mayar da yara makarantu, don kauce wa faɗawa cikin ayyukan ta’addanci.
Sakataren dindindin na Ma’aikatar Harkokin Jin-ƙai da Kula da Bala’o’i, Mista Olu Bunmi Olusanya, ya bayyana cewa tallafin ya yi daidai da gyare-gyaren da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa, waɗanda suka mayar da hankali kan gaskiya da adalci wajen zaɓen masu amfana, da ingantaccen isar da tallafi kai tsaye ga waɗanda suka fi buƙata cikin mutunci da kan lokaci.
Shi ma Kwamishinan Harkokin Jin-ƙai da Kula da Bala’o’i na Jihar Niger, Ibrahim Inga, ya ce duk da nasarorin da ma’aikatar ta samu tun bayan kafuwarta kimanin shekaru uku da suka gabata, tana fuskantar ƙalubale da dama sakamakon ƙarancin kuɗaɗe da yawaitar bala’o’i. Don haka ya buƙaci ƙarin tallafi daga Gwamnatin Tarayya, tare da yin kira ga masu amfana da kada su sayar da kayan tallafin a kasuwa.
Aliyu Lawal
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
