Connect with us

Labarai

Taraba Ta Kaddamar da Rarraba Kayan Aikin A Kananan Hukumomi 16

Published

on

Hukumar Kula da Ci gaban Kiwon Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Taraba ƙarƙashin Shirin IMPACT, ta ƙaddamar da rarraba kayan aikin lafiya da babura ga jami’an sa ido da tantance ayyuka (M&E) a kananan hukumomi 16 na jihar.

An gudanar da bikin ƙaddamarwar ne a ranar Alhamis, 26 ga Fabrairu, 2026, a Jalingo, da nufin ƙarfafa tsarin sa ido da inganta bayar da ayyukan kiwon lafiya a matakin ƙasa.

An samar da kayan ne ta hannun Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Taraba tare da tallafin World Bank Nigeria, ƙarƙashin Shirin IMPACT.

Baburan an ware su ne domin jami’an sa ido da tantance ayyuka na kananan hukumomi, yayin da kayan aikin lafiyar kuma za su taimaka wajen inganta ayyukan kiwon lafiya a matakin farko a yankunan karkara.

Da yake ƙaddamar da shirin, Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Bordiya Buma, ya ce wannan tallafi zai ƙara tabbatar da gaskiya da riƙon amana, da ƙarfafa sa ido, tare da inganta sakamakon ayyukan kiwon lafiya, musamman a yankunan karkara da wuraren da ke da wahalar isa.

A nasa jawabin, Manajan Shirin IMPACT a jihar, Dakta Ubanus Ezekiel, ya bayyana cewa tun bayan fara cikakken aiwatar da shirin a watan Janairun bara, an samu gagarumin ci gaba.

Shi ma Babban Kwararren Lafiya kuma Jagoran Tawagar Shirin IMPACT na Bankin Duniya a ofishin Abuja, Dakta Onoriode Ezire, ya yabawa Gwamna Agbu Kefas bisa bai wa kiwon lafiyar matakin farko muhimmanci, yana mai cewa ƙarfafa kananan hukumomi na da matuƙar tasiri wajen inganta ayyukan kiwon lafiya.

Da yake magana a madadin shugabannin kananan hukumomi, Shugaban ALGON na Jihar Taraba, Mista Moses Maihankali, ya ce Shirin IMPACT ya inganta kayan aikin asibitoci a kananan hukumomi 16 na jihar.

A wata hira da aka yi da ita, Mai Kula da Shirin IMPACT a matakin ƙasa na Bankin Duniya a Najeriya, Dakta Amina Abdula-One, ta yi alƙawarin ci gaba da tallafa wa Gwamnatin Jihar Taraba domin cimma burinta na samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya ga al’umma a matakin ƙasa.

Rediyon Najeriya ya lura cewa wasu daga cikin shugabannin kananan hukumomi, ciki har da Shugaban Karamar Hukumar Jalingo, Mista Nuru Dantsoho, sun riga sun karɓi kayayyakinsu domin rabawa.

Haka kuma, a yayin bikin, ɗaya daga cikin jami’an sa ido da ya ci gajiyar shirin ya gwada ɗaya daga cikin sabbin baburan da aka raba.

Sani Sulaiman

Labarai

Labarai2 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi1 week ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Mafi Shahara