Labarai
Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
Daga Shamsuddeen Mannir Atiku
Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da Kudirin Kasafin Kuɗin Ƙananan Hukumomi na shekarar 2026 ya zama doka, inda ta sahale kuɗi sama da Naira Biliyan 152 ga ƙananan hukumomi 23 na jihar.
Shugaban Majalisar, Yusuf Dahiru Liman, ya bayyana cewa kuɗaɗen da aka amince da su za su taimaka matuƙa wajen bunƙasa tattalin arziki da inganta ayyukan more rayuwa a faɗin yankunan ƙananan hukumomi.
Ya kuma bayyana kyawar fatar cewa aiwatar da kasafin yadda ya kamata zai inganta rayuwar jama’a musamman a matakin gunduma.

Tun da farko, da yake gabatar da rahoton Kwamitin Majalisar na Kasafi da Aiwatarwa, Shugaban Kwamitin, Shehu Yunusa Pambegua, ya bayyana cewa shugabannin ƙananan hukumomi 23 sun gurfana a gaban kwamitin domin kare yadda suka aiwatar da kasafin shekarar 2025 tare da gabatar da kasafin shekarar 2026.
Ya ƙara da cewa bayan tantancewa da gyare-gyaren cikin gida, kwamitin ya amince da adadin kasafin kamar yadda aka aiko da shi, wanda ya haura naira biliyan 152.
A cewarsa, kuɗaɗen gudanar da al’amuran yau da kullum sun kai sama da Naira Biliyan 91 da miliyan 500, yayin da kuɗaɗen manyan ayyukan raya ƙasa suka zarce Naira Biliyan 61.4.

Pambegua ya buƙaci shugabannin ƙananan hukumomi da su tabbatar da aiwatar da kasafin cikin tsari da gaskiya domin cimma muradun al’umma, musamman ganin cewa lokacin zaɓe na tafe.
Ya kuma lura cewa Gwamnan Jihar ya sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora mishi ta hanyar gabatar da kudirin kasafin, yana mai jaddada cewa yanzu aiki ya rataya a wuyan shugabannin ƙananan hukumomi su aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa da za su ɗaga martabar al’ummomin yankunan karkara.
Haka zalika, ya bayyana Gwamnan a matsayin mai kaunar raya karkara wanda ke bai wa manufofi da shirye-shiryen da ke bunƙasa tattalin arziki a yankunan karkara muhimmanci.
An amince da kudirin ne bayan ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Ikara, Hassan Mohamed, ya gabatar da bukatar hakan, wanda kuma ɗan majalisar mai wakiltar mazaɓar Birnin Gwari, Shehu Hassan, ya mara masa baya.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
