Connect with us

Labarai

Kano Tana Karfafa Shirin Rigakafi Ga Yaran da Ba Su Karbi Allura Ba

Published

on

A wani yunkuri na ƙarfafa shirin rigakafin yau da kullum, Hukumar Kula da Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Kano ta gudanar da wata ganawa ta musamman da manyan masu kula da cibiyoyin lafiya da Jami’an Rigakafi na yau da kullum daga kananan hukumomi 15 da aka gano suna da yawan yaran da ba su taba karɓar ko wace allurar rigakafi ba.

Taron wanda aka gudanar a hedikwatar hukumar da ke Na’ibawa, ya samu jagorancin Darakta Janar, Farfesa Salisu Ahmed, wanda ya sake jaddada kudirin gwamnatin jihar na tabbatar da an kai wa kowane yaro da aka bari a baya rigakafi.

Tattaunawar ta mayar da hankali ne kan sabon tsarin na rigakafin yau da kullum, wanda aka tsara domin ganowa, bibiyar su da kuma yi wa yaran da ba su taba karɓar allura ba ko kuma wadanda ba su kammala jadawalin rigakafinsu ba allurar da ta dace, musamman a al’ummomin da matsalar ta fi kamari.

Farfesa Ahmed ya bayyana cewa kawar da yankunan da ke da yawan yaran da ba a musu alluran ba na daga cikin manyan manufofin lafiyar al’umma, inda ya bukaci shugabannin cibiyoyin lafiya su tabbatar da ingancin bayanai, tsauraran sa ido a filin aiki, da kuma ƙarfafa wayar da kan al’umma domin ƙara yawan masu karɓar rigakafi.

Daya daga cikin muhimman batutuwan da aka tattauna a taron shi ne fayyace rawar da kowane mamba na tawagar kananan hukumomi zai taka, domin tabbatar da hadin kai, ɗaukar alhaki, da kuma sa ido kan yadda ake aiwatar da shirin yadda ya kamata.

Darakta Janar ya kuma bukaci mahalarta taron su nuna jajircewa da kishin aiki, su ƙarfafa tsarin kulawa da sa ido, tare da samar da sakamakon da zai nuna irin jagorancin da Jihar Kano ke da shi a fannin gyaran tsarin kula da lafiyar matakin farko.

Shirin na samun tallafi daga gidauniyar Bill & Melinda Gates ta hannun abokan hulɗa masu aiwatarwa, domin rage gibin rigakafi da kuma kare lafiyar kowane yaro a Jihar Kano.

Hukumar ta kuma jaddada cewa ci gaba da irin wannan hadin gwiwa a matakin kananan hukumomi na da matukar muhimmanci wajen cimma burin kasa na rigakafi tare da tabbatar da cewa babu wani yaro da za a bari a baya.

Khadijah Aliyu/Kano

Labarai

Labarai24 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai1 day ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara