Labarai
Gwamnatin Kano Ta Yaba da Aikin Kare Zaizayar Kasa da ke Gudana a Sumaila
Daga Khadijah Aliyu
Kwamishinan Ma’aikatar Samar da Kayayyakin Gwamnati da Kula da Ayyuka ta Jihar Kano, Nura Ma’aji, ya ziyarci garin Rimi da ke Karamar Hukumar Sumaila don duba aikin gina bututun ruwa da kare zaizayar kasa.
Aikin wanda ke karkashin Ma’aikatar Muhalli na da nufin kare gidaje, gonaki, hanyoyi da unguwanni daga ambaliyar ruwa da kwari. Ya kuma shafi yankuna daga Makarantar Firamare ta Rimi zuwa bakin kogi da unguwannin dake kusa.
Kwamishinan ya yaba wa injiniyoyi da ‘yan kwangila bisa yadda aikin ke tafiya daidai da jadawalin da aka tsara. Ya kuma jaddada muhimmancin sa ido don ganin an samu aiki mai inganci.
Mazauna garin Rimi sun nuna godiyarsu, tare da bayyana cewa aikin zai kawo sauki ga matsalolin kwari da ruwan sama da suka dade suna fuskanta.
Wannan aiki wani bangare ne na shirin Abba Kabir Yusuf na bunkasa muhalli da rayuwar al’umma a Kano.
Hakazalika Kwamishinan ya duba ayyuka 10 a Kananan Hukumomin Takai da Sumaila, ciki har da tituna masu tsawon kilomita 5, da aikin na biyu na rukunin azuzuwan Kwankwasiyya Gida-Gida.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai21 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai24 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
