Labarai
Jam’iyyar APC ta Zabi Sabbin Shugabanninta a Jihar Zamfara
Daga Aminu Dalhatu
Jam’iyyar APC ta gudanar da tarukan zaɓen shugabanni na mazabu da na ƙananan hukumomi cikin nasara a dukkan mazabu 147 da ƙananan hukumomi 14 na Jihar Zamfara, inda aka fitar da shugabannin jam’iyyar ta hanyar sulhu.
An gudanar da tarukan cikin kwanciyar hankali, kuma an bayyana su a matsayin masu tsari da nagarta, tare da halartar masu ruwa da tsaki da mambobin jam’iyyar daga sassa daban-daban na jihar.
Da yake zantawa da manema labarai a Gusau, shugaban kwamitin gudanar da tarukan, Babande Babakura Imam, ya ce an gudanar da aikin cikin nasara ba tare da wata tangarda ba.
Imam ya bayyana cewa tarukan na mazabu da ƙananan hukumomi sun samu halartar jama’a da yawa, inda aka sami dukkan shugabanni ta hanyar sulhu da amincewar mambobin jam’iyyar.
Ya ce, “Jami’an HukumarZabe mai Zaman Kanta ta kasa(INEC), da jami’an tsaro, da wakilan jam’iyyar APC daga sakatariyar ƙasa da ke Abuja, da kuma wakilan APC na jiha ne suka sanya ido kan yadda aka gudanar da tarukan.”
A cewarsa, tarukan ƙananan hukumomi sun fitar da shugabannin APC a dukkan ƙananan hukumomi 14, ciki har da shugabanni, sakatarori da sauran jami’ai.
Shi ma da yake jawabi, shugaban APC na Jihar Zamfara, Alhaji Tukur Danfulani, ya bayyana nasarar gudanar da tarukan a matsayin abin farin ciki ga jam’iyyar.
Danfulani ya yabawa kwamitin tarukan bisa bin ƙa’idojin jam’iyyar yadda ya kamata, wajen gudanar da aikin a duk faɗin jihar, yana mai jaddada cewa APC na da ƙudurin tabbatar da gaskiya da haɗin kai.
Shugaban jam’iyyar ya kuma nuna kwarin gwiwa cewa APC na da haɗin kai gabanin zaɓuka masu zuwa a jihar, yana mai cewa fitowar sabbin shugabanni zai ƙara ƙarfafa tsarin jam’iyyar.
“Wannan ci gaba alama ce cewa APC ta shirya tsaf domin ƙwato jihar Zamfara tare da yin aiki domin sake zaɓen Bola Ahmed Tinubu da dukkan ‘yan takarar APC a zaɓen shekarar 2027,” in ji Danfulani.
Ya kuma bayyana gamsuwarsa da yadda mambobin jam’iyyar suka halarci tarukan da kuma yadda aka gudanar da su cikin tsari da lumana a faɗin jihar.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
