Connect with us

Labarai

An Buɗe Gadar Ƙarfafa Cibiyar Wutar Lantarki A Kano

Published

on

An buɗe sabuwar Gadar TRC da aka gina a wurin tashar samar da wutar lantarki ta ruwa mai ƙarfin megawatt 6 (6MW) a Challawa, domin amfanin jama’a.

 

Gadar za ta sauƙaƙa zirga-zirga tare da ƙarfafa haɗin kai tsakanin garin Turawa, ƙananan hukumomin Karaye da Kiru, da ma sauran al’ummomin da ke makwabtaka da su a Jihar Kano.

 

An jagoranci bikin ƙaddamar da gadar ne ta hannun Kwamishinan Ma’aikatar Wutar Lantarki da Makamashi, Gaddafi Sani Shehu, wanda ya bayyana gadar a matsayin muhimmin aikin more rayuwa da zai inganta harkokin sufuri tare da bunƙasa ayyukan tattalin arziƙi a yankin.

 

Ya kuma bayyana cewa gina Gadar TRC ya yi daidai da manufofin ci gaban Gwamna Abba Kabir Yusuf, waɗanda suka fifita faɗaɗa ayyukan more rayuwa da samar da ci gaba mai ɗorewa a fannin tattalin arziƙi a faɗin jihar.

 

A nasa jawabin, Manajan Daraktan Kamfanin lantarki na Kano, Injiniya Ado Ibrahim Doguwa, ya ce gadar za ta sauƙaƙa zirga-zirgar mutane da kayayyaki tare da haɓaka harkokin kasuwanci a yankin.

 

Shi ma Manajan Aikin, Injiniya Shailendra Singh, ya tabbatar da kammala gadar a matsayin wani ɓangare na aikin samar da wutar lantarki ta ruwa na Challawa mai ƙarfin 2x3MW.

 

Ya ƙara da cewa ana sa ran aikin samar da wutar lantarki na Challawa 2x3MW zai ci gaba da samar da wuta ga Gwamnatin Jihar Kano nan da ƙarshen watan Mayu 2026 ko farkon watan Yuni 2026, lamarin da zai zama wani muhimmin mataki wajen ƙarfafa cibiyar samar da wutar lantarki a jihar.

 

Kwamishinan ya samu rakiyar Manajan Daraktan Hukumar Samar da Wutar Lantarki ta Karkara ta Jihar Kano (REB), Injiniya Bala Dambatta, tare da sauran manyan jami’ai daga Ma’aikatar Wutar Lantarki da Makamashi.

 

Khadijah Aliyu

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara