Labarai
Wata Kungiya Ta Raba Kayan Abinci Ga Fursunoni A Wamba
Wata ƙungiyar agaji mai suna Islamic Society of Eggon-land (ISE) ta bai wa fursunoni da ke Cibiyar Gyaran Hali ta Wamba kayan abinci na sahur da buɗa-baki da darajarsu ta kai miliyoyin naira.
Yayin da yake miƙa kayan, Babban Sakataren ƙungiyar, Alhaji Umar Abdullahi Galle, ya bayyana cewa wannan tallafi wani ɓangare ne na al’adar da ƙungiyar ke yi a duk watan Ramadan domin tallafa wa ƙoƙarin gwamnati tare da kyautata jin daɗin fursunoni da inganta lafiyarsu yayin da suke zaman hukunci.
Ya ce manufar wannan tallafi ba wai rage ƙimar abin da gwamnati ke yi ba ne, sai dai don ƙara musu farin ciki da jin daɗi. Ya jaddada cewa kayan abincin ba na Musulmi kaɗai ba ne, an tanade su ne domin dukkanin fursunoni da ke zaman hukunci, kamar yadda kowa ke buƙatar buɗa-baki a wannan wata mai alfarma.
Alhaji Umar Abdullahi Galle ya kuma roƙi shugabannin cibiyar da su yi amfani da kayan yadda ya dace, domin ci gaba da kyakkyawar dangantaka da ake da ita. Ya tunatar da cewa sun ziyarci cibiyar a bara, inda suka samu kyakkyawan rahoto daga fursunoni kan yadda aka sarrafa tallafin da aka bayar a wancan lokaci, tare da kira ga shugabannin da su ci gaba da wannan kyakkyawan tsari.
Da yake karɓar kayan, Shugaban Cibiyar Gyaran Hali ta Wamba, John Ali-Bando, ya nuna godiya ga ƙungiyar Islamic Society of Eggon-land (ISE) bisa wannan karamci, tare da alƙawarin amfani da kayan yadda ya dace domin amfanin fursunonin.
Ya kuma yi kira ga sauran ƙungiyoyin agaji da na addini da su yi koyi da irin wannan aiki domin taimaka wa masu buƙata da inganta yanayin cibiyoyin gyaran hali a ƙasar.
COV/Aliyu Muraki/Lafia.
-
Labarai5 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha4 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai4 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai3 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai3 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai3 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai3 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
-
Labarai3 days ago2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro
