Labarai
NUJ ta Jihar Neja Ta Taya Gwamna Bago Murnar Cika Shekara 52
Majalisar Nigeria Union of Journalists (NUJ) reshen Jihar Niger ta taya Gwamnan jihar, Mohammed Umar Bago, murnar cika shekaru 52 da haihuwa.
A cikin saƙon taya murna da aka fitar a Minna, Sakataren NUJ na jihar, Kwamared Usman Chiji, ya bayyana cewa cika shekaru 52 a duniya da kusan shekaru uku a kan mulki, rayuwar Gwamna Bago ta nuna alamar falala da rahamar Allah.
Sanarwar ta yabawa gwamnan bisa ƙoƙarinsa na kawo sauyi ta hanyar bai wa muhimman fannoni fifiko domin cimma manufar “Sabuwar Neja”.
Ta kuma jaddada cewa salon rayuwarsa na abin koyi da ƙwarewarsa a fannin gudanarwa sun ba shi karɓuwa da girmamawa, lamarin da ya kai ga zaɓensa sau uku a jere a matsayin ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Chanchaga, kafin daga bisani a zaɓe shi Gwamna a shekarar 2023.
Sanarwar ta ƙara da cewa a matsayinsa na mai kishin shugabanci nagari, Gwamna Bago ya ƙaddamar da manufofi da shirye-shirye da suka shafi rayuwar al’umma kai tsaye, ciki har da gagarumin aikin sabunta birane ta hanyar gina hanyoyi masu tsawon kilomita 556 a dukkanin ƙananan hukumomi 25 na jihar.
Yayin taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa, NUJ ta tabbatar da ci gaba da ba da goyon baya da haɗin kai, tare da jaddada buƙatar ƙara ƙarfafa kyakkyawar alaƙa da ke tsakanin ‘yan jarida da gwamnati.
Majalisar ta kuma yi addu’ar Allah Ya ƙara wa Gwamna Umar Bago shekaru masu yawa cikin ƙoshin lafiya, jarumta da ƙarfi domin cika alƙawuran da ya ɗauka ga al’ummar jihar.
PR Aliyu Lawal.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
