Connect with us

Labarai

Hukumar Raya Kogin Benuwe Ta Bullo da Sabuwar Fasahar Kare Hanyar Ban-ruwa a Tafkin Geriyo

Published

on

Daga Yusuf Zubairu/Abubakar Hamza 

Shugaban Hukumar Raya Kogin Benuwe Dakta Mahmud Sanusi Mohammed, ya bullo da wata fasaha mai sauki da za ta kare hanyar shiga aikin ban-ruwa na Tafkin Geriyo daga zaizayewa  a lokacin damina.

Wannan shiri ya biyo bayan ziyarar duba aikin samar da ruwa ga gonaki  da ya kai, inda ya tantance matsalolin da ke haddasa zaftarewar hanyoyi musamman hanyar da ake wannan aiki.

   A tsakiya, Shugaban Hukumar Raya Kogin Benuwe ne Dakta Mahmud Sanusi Mohammed

Domin magance matsalar, hukumar na amfani da wata sabuwar hanya wadda ta haɗa da amfani da tsofaffin tayoyin motoci da aka cika da dakakken dutse da tsakuwa. Ana jera tayoyin ne ta yadda za su matse juna, su zama wani gini mai ƙarfi domin hana zaizayar ƙasa da kuma daidaita magudanar ruwa.

An tsara wannan dabara ce domin rage ƙarfin ruwan da ke gudana a saman ƙasa, ƙarfafa ƙasa, da kuma hana zaftarewar hanya a lokacin damina.

Jami’ai sun bayyana cewa wannan hanya da aka bullo da ita tana da amfani matuka ga muhalli, domin tana ƙarfafa sake amfani da kayayyakin shara,  tare da rage kuɗaɗen da ake kashewa wajen yin gyara.

Haka kuma ana sa ran wannan tsari zai ƙara ingancin hanyar shiga wurin tare da tabbatar da samun damar zuwa wuraren ban-ruwa a kowane lokaci na shekara.

Shugaban Hukumar ya shaidawa Rediyon Najeriya cewa,halin yanzu wannan aiki a cigaba da gudana, wanda ke nuna ƙudurin shugabancin hukumar na samar da mafita da za ta kare muhimman kayayyakin more rayuwa, tare da ƙarfafa ayyukan ban-ruwa masu dorewa a yankin.

Labarai

Labarai6 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai9 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai7 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai7 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai7 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai7 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai7 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara