Connect with us

Labarai

Gwamnatin Tarayya ta Bada Tallafin Kayayyakin Aiki Gona ga Ƙananan Manoma a Jigawa

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria

Gwamnatin tarayya ta ce sauya fasalin bangaren noma a Najeriya ta hanyar bai wa samar da wadataccen abinci muhimmanci.

Ministan Noma da Wadata Kasa da Abinci, Sanata Abubakar Kyari, ya bayyana hakan yayin rabon kayayyakin noma ga kananan manoma a Dutse, babban birnin jihar Jigawa.

Ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya na aiwatar da gyare-gyaren tattalin arziki da dama domin bunkasa samar da ayyukan yi, da kuma rage tsadar rayuwa.

A cewarsa, Ma’aikatar Noma da  ta kaddamar da shirye-shirye da ayyuka da dama domin magance wasu matsalolin da manoma ke fuskanta, tare da tabbatar da wadatar abinci, samun sa cikin sauki, da kuma rage tsadarsa ga dukkan ‘yan Najeriya.

Ministan, wanda Daraktan Sashen Noman Lambu na Ma’aikatar Noma da Wadata Kasa da Abinci ta Tarayya, Alhaji Yarima Uba, ya wakilta, ya ce sun kuduri aniyar tabbatar da cewa dukkan shirye-shirye da tsare-tsaren bangaren noma na wannan gwamnati sun yi daidai da manufofin shugaban kasa.

⁹

Sanata Abubakar Kyari ya kara da cewa, gwamnatocin tarayya da na jihohi na ci gaba da hadin gwiwa domin magance dukkan matsalolin da ke shafar wadatar abinci.

A cewarsa, ma’aikatar na da kudurin karfafa hadin gwiwa da kungiyoyi da kamfanoni masu zaman kansu domin kara inganta kokarin tabbatar da wadatar abinci, bunkasar tattalin arziki, samar da ayyukan yi da rage talauci.

Ya nuna cewa, ma’aikatar ta tanadi aiwatar da tsare-tsare na gajeren lokaci da hanyoyin tallafi domin rage tsadar muhimman kayayyakin noma, tare da saukaka samunsu ga manoma ta hanyar tsari mai inganci da rikon amana.

Abubakar Kyari ya bukaci wadanda suka amfana da kayayyakin da su yi amfani da su yadda ya dace domin samar da karin abinci ga kasa.

Ya ce “Babban abin da muka sa a gaba shi ne saukaka samar da kayayyakin noma da na’urorin aikin gona masu inganci ga kananan manoma da tsadar wadannan kayayyaki ke hana su samun su, wanda hakan ke bukatar tallafi.”

Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa kayayyakin da aka rabawa manoman kyauta sun hada da injinan noma da ake kerawa a nan gida Najeriya,  magungunan kashe ciyawa, takin zamani na ruwa, na’u’rorin feshin magani, injinan famfon ruwa, da sauransu.

An yi rabon kayayyakin ne ta hannun kungiyoyin masu noma amfanin gona daban-daban, kungiyoyin hadin gwiwar manoma, manoma masu bukata ta musamman da kuma ‘yan gudun hijira.

Labarai

Labarai16 hours ago

Sauye-sauyen Da Tinubu Ya Samar Ya Haifar Da Cigaba A Jihohi – Namadi

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan matakan da...

Labarai19 hours ago

Jigawa Ta Yi Nazarin Sabbin Tsare-tsaren Masaukin Alhazai A Saudiyya

Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce tana nazarin hanyoyin inganta jin daɗin alhazai...

Labarai2 days ago

Kano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400

Daga Khadijah Aliyu  Wata kotu a Jihar Kano ta bayar da umarnin lalata buhunan fulawa sama da 400 da suka...

Labarai3 days ago

Tinubu Ya Jaddada Ƙudurin Samar Da Ci Gaba A Jigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da...

Labarai3 days ago

Shugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus

Daga Isma’il Adamu  Babban Manajan gidan talabijin na Jihar Katsina (KTTV), Abba Zayyan, ya miƙa takardar murabus daga muƙaminsa a...

Labarai3 days ago

Namadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kai musu...

Labarai3 days ago

Arewa Za Ta Saka Wa Tinubu Da Ruwan Kuri’a A 2027- Yari

Daga Usman Muhammad Zaria  Daraktan Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce...

Labarai3 days ago

Shettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bukaci ’yan Najeriya da su goyi bayan sake zaɓen Shugaba...

Labarai4 days ago

Jigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz

Daga Usman Muhammad Zaria Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan harkokin yada labarai da wayar dan...

Labarai4 days ago

Majalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027

Daga Khadijah Aliyu  Majalisar Dokokin Jihar Kano na shirin karɓar daftarin kasafin kuɗin shekarar 2027 daga Gwamna Abba Kabir Yusuf...

Mafi Shahara